An yankewa wasu masu Coronavirus hukuncin kisa saboda sunki bin umarnin gwamnati na killace kansu a gida

An yankewa wasu masu Coronavirus hukuncin kisa saboda sunki bin umarnin gwamnati na killace kansu a gida

Hukumar 'yan sandan kasar Afrika ta Kudu ta zargi wasu mutane biyu da laifin kisan kai, bayan an tabbatar da cewa suna da cutar Coronavirus kuma suka ki yadda su killace kansu a gida

Ministan 'yan sanda na kasar Bheki Cele shine ya bayyana haka a ranar Laraba a lokacin wata hira da yayi da manema labarai, inda ya ce: "idan kuka karya wannan dokar sai kayi zaman gidan yari na wata shida ko kuma a cika tara."

"Yanzu haka mun kama mutane biyu wadanda suka karya dokar bayan an sanar da su cewa kada su karya.

An yankewa wasu masu Coronavirus hukuncin kisa saboda sunki bin umarnin gwamnati na killace kansu a gida

An yankewa wasu masu Coronavirus hukuncin kisa saboda sunki bin umarnin gwamnati na killace kansu a gida
Source: Facebook

"Saboda haka ba wai tatsuniya bace dan mun ce muku gwamnati za ta dauki doka mai tsauri akan wannan lamarin."

Na farko wani dan shekara 52 ne wanda yake da shagon gyaran jiki, an tabbatar da yana da cutar a ranar 18 ga watan Maris, sannan aka umarce shi ya killace kanshi na tsawon kwanaki 14.

Kakakin rundunar 'yan sanda, Vish Naidoo ya ce mutanen yankin ne suka kai rahoto bayan sun ga mutumin ya fito yana yawo a ranar Talata a yankin KwaZulu-Natal.

Mutum na biyu kuma an tabbatar da cutar a jikin shi bayan yaje yawon bude ido wajen shakatawa na Kruger National Park.

Naidoo ya ce mutumin yaki jin umarnin gwamnati ya fita daga otel din shi ya tafi wani gari dake makwabtaka da wajen, inda ya hadu da mutane masu tarin yawa.

A yanzu haka dai kasar Afrika ta Kudu na dauke da mutane 709 da suke da cutar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel