Sowore ya zargi gwamnatin Buhari da kokarin kamashi ta sanya masa cutar Coronavirus

Sowore ya zargi gwamnatin Buhari da kokarin kamashi ta sanya masa cutar Coronavirus

Omoyele Sowore, ya zargi gwamnatin tarayya da kokarin sanyawa a kamashi ta sanya masa cutar Coronavirus da ta addabi duniya baki daya

A wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na Facebook jiya da dare, Sowore ya bayyana cewa wannan kokarin kama shi da gwamnatin tarayyar take yi yana da nasaba da rahoton da jaridar shi ta Sahara Reporters ta wallafa na cewa shugaban ma'aikata na gwamnatin shugaba Buhari, Abba Kyari na dauke da cutar Coronavirus.

Ya ce: "Jama'a yana da matukar muhimmanci na sanar da ku halin da muke ciki, saboda kwanaki masu zuwa za su zama ciki wahala, amma komai zai daidaita.

"Bayana rahoton da Sahara Reporters ta wallafa na cewa shugaban ma'aikata na Najeriya, Abba Kyari na dauke da cutar Coronavirus, da kuma rahoton da muka bayyana na yadda sakacin gwamnatin Najeriya ya jawo mana shigowar wannan cuta, yanzu gwamnatin Buhari ta aika wasu manyan mutane ga alkalin alkalai akan ya bada umarnin a kama ni.

KU KARANTA: Kamfanin jirgin sama na Dana zai bawa Najeriya jirgi kyauta da za a dinga daukar kayan tallafi na Coronavirus

"Kotun ma baki daya suna hutu saboda matsalar Coronavirus. Mun samu wannan labarin ne daga bakin lauyan mu mintuna kadan da suka wuce. Yanzu suna so suyi amfani da sojoji wajen yin duk abinda suke so. Shirin su shine kotu ta basu dama sai su turo sojoji gidana su kamani su kai ni barikin sojoji su azabtar dani ko kuma su sanya mini cutar Coronavirus.

"Ba wai ina sanar da haka bane saboda na tsorata wasu, ina sanar daku ne domin abokanai na su san cewa wahala na zuwa nan gaba kadan."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Nigeria

Online view pixel