Kamfanin jirgin sama na Dana zai bawa Najeriya jirgi kyauta da za a dinga daukar kayan tallafi na Coronavirus

Kamfanin jirgin sama na Dana zai bawa Najeriya jirgi kyauta da za a dinga daukar kayan tallafi na Coronavirus

Kamfanin jirgin sama na Dana Air ya bayar da jirgi, ma'aikata da duk wani abu da ake bukata ga gwamnatin Najeriya a kokarin da kamfanin yake na taimakawa wajen rage yaduwar cutar Coronavirus

Shugaban fannin sadarwa na kamfanin, Kingsley Ezenwa, shine ya bayyana haka a yau Juma'ar nan a jihar Legas.

Mr Ezenwa ya bayyana hakane a wata takarda da ya aikawa ministan sufurin jiragen sama na kasa, Sanata Hadi Sirika, kamfanin Dana Air ya nuna cewa zai taimaka da jirgi da kuma kayan taimako ga jihohin kasar nan a duk inda ake bukatarsu.

A takardar da shugaban kamfanin ya sanyawa hannu, Jacky Hathiramani ya bayyana cewa kamfanin ya gama shiri wajen bawa Najeriya tallafin jirgin sama, kayan tallafi da kuma ma'aikatan jirgi domin rage yaduwar cutar a fadin kasar.

Kamfanin jirgin sama na Dana zai bawa Najeriya jirgi kyauta da za a dinga daukar kayan tallafi na Coronavirus

Kamfanin jirgin sama na Dana zai bawa Najeriya jirgi kyauta da za a dinga daukar kayan tallafi na Coronavirus
Source: UGC

Mr Hathiramani ya ce: "Wannan matsalace da ta shafi duniya baki daya, saboda haka lokaci yayi da kowannen mu zai yi iya bakin kokarinshi wajen ganin ya rage yaduwar cutar a kasashen mu.

"Bana jin dadi ko kadan da yadda ake ta faman samun yaduwar cutar a Najeriya, hakan ya sanya kuma muka yanke hukuncin dakatawa da aiki na tsawon kwanaki 14.

"Taimakon da zamu bayar a matsayin mu na kamfanin jirgi zai zama kawai kari ne akan abinda gwamnati take yi wajen rage yaduwar cutar.

Mr Ezenwa ya ce kamfanin Dana Airline yana daya daga cikin manyan kamfanin jiragen sama na Najeriya da yake da jirage guda 9 da yake jigilar fasinjoji daga Legas, Abuja, Fatakwal, Uyo da kuma Owerri.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel