Gwaji ya nuna Coronavirus ta kama Likitocin Kungiyar Barcelona

Gwaji ya nuna Coronavirus ta kama Likitocin Kungiyar Barcelona

A halin yanzu da Kasashen Duniya su ke ta fama da cutar Coronavirus, a kasar Sifen lamarin ya yi kamari inda mutane fiye da 4, 000 su ka rasa rayukansu a cikin 'yan watanni.

Rahotanni sun bayyana cewa wannan cuta ta shiga kungiyar kwallon Barcelona. Wannan ne karon farko da wani daga cikin Ma’aikatan wannnan kungiya ya kamu da cutar.

Likitocin kungiyar kwallon kafan har biyu ne su ka kamu da wannan mummunar cuta da yanzu alkaluma su ka tabbatar da cewa ta kashe akalla mutane 24, 000 a Duniya.

Bayan an yi wa wadannan Likitoci gwaji, an tabbatar da cewa su na dauke da wannan kwayar cuta. A kasar Sifen, kimanin mutane 50, 000 ne su ka kamu da wannnan cutar.

Jaridun Daily Star ta Turai da La Vanguardia ta kasar Sifen sun rahoto wannan labari. Manyan Malaman lafiyan kungiyar Barcelonan ne su ka kamu da cutar ta COVID-19.

KU KARANTA: Cutar COVID-19 ta na neman ta ci Shugaban farko a Duniya

Ramon Canal wanda shi ne shugaban ma’aikatan lafiyar kungiyar ya kamu da wannan cuta. Canal babban Masani ne daga Yankin Kataloniya wanda ya ke aiki da kungiyar.

Haka zalika wannan cuta mai jawo wahalar mumfashi a mashako ta kama Josep Antoni Guttierez. Wadannan su ne mutanen farko da su ka fara kamu da cutar a kungiyar.

Mista Antoni Guttierez shi ne babban Likitan da ke kula da ‘Yan wasan kwallon hannu na kungiyar Barcelona. A halin yanzu dai an kai su asibitin Sifen domin su yi jinya.

Kungiyar ta Barcelona ba ta bayyana ainihin halin da ake ciki ba, sai dai rahotanni sun tabbatar da cewa ana sa ran wadannan Bayin Allah za su samu sauki a gadon asibiti.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel