Yan ta’addan Boko Haram sun ji a jikinsu yayin da Sojoji suka daka musu wawa a Borno

Yan ta’addan Boko Haram sun ji a jikinsu yayin da Sojoji suka daka musu wawa a Borno

Shelkwatar tsaro ta kasa ta sanar da wata gagarumar nasara da dakarun Sojin Operation Lafiya Dole suka samu a wani samame da suka kai a wani sansanin samar da horo da na Boko Haram da mayakan ISWAP.

Kamfanin dillancin labarun Najeriya ta ruwaito daraktan watsa labaru na shelkwatar, Birgediya Janar Bernard Onyeuko ne ya bayyana haka cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Alhamis a babban birnin tarayya Abuja.

KU KARANTA: Majalisar wakilai ta bayar da kwangilar sayen motocin alfarma guda 400

A cewar Onyeuko, hadakan dakarun rundunar sojan kasa da na rundunar Sojan sama ne suka kai farmakin a ranar Laraba 25 ga watan Maris bayan samun sahihan bayanan sirri da suka tabbatar da tattaruwar yan ta’adda a sansanin dake kauyen Matuku a Arewacin Borno.

“Yan ta’addan ISWAP suna amfani da sansanin wajen ajiya kayan aikinsu tare da horas da mayakansu, wannan ne yasa Operation Lafiya Dole ta aika da jiragen yaki zuwa sansanin, inda suka yi musu ruwan bamabamai da suka halaka duk wanda ke ciki tare da lalata sansanin.” Inji shi.

Daga karshe Onyeuko ya nanata manufar rundunar Sojan sama na kawo karshe yakin da take yi da yan ta’addan Boko Haram ta hanyar gamawa da yan ta’addan tare da tabbatar da tsaron al’ummar yankin da dukiyoyinsu.

A wani labarin kuma, kafatanin rundunonin Najeriya na zaune cikin shirin ko-ta-kwana tare da aiki da cikawa domin dabbaka umarnin shugaban kasa Muhammadu Buhari na garkame Najeriya da zarar ya bayar da umarnin yin hakan sakamakon yaduwar annobar Coronavirus.

Wata majiya daga cikin manyan jami’an Sojin kasar nan ta shaida cewa an aika ma kowanne rukunin Sojin Najeriya sako daga shelkwatar tsaro ta kasa a kan su kasance cikin shirin ko-ta-kwana, a ranar Talata.

Haka zalika wasu kafafen sadarwa na yanar gizo sun wallafa wasu takardu da suka yi ikirarin sun fito ne daga shelkwatar tsaro ta kasa dake bayyana shirin Sojoji na mamaye kasar cikin kankanin lokaci domin tabbatar da jama’a kowa ya zauna a gidansa don kauce ma yaduwar annobar.

Wannan rahoto ya fito ne bayan kimanin sa’o’i 72 da ministan watsa labaru, Lai Muhammad ya bayyana cewa kwamitin da shugaban kasa ya kafa don kare yaduwar cutar ta bashi shawarar daukan wasu tsauraran matakai.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel