Yadda LUTH suka ce mai cutar COVID-19 ya koma gida don babu gado

Yadda LUTH suka ce mai cutar COVID-19 ya koma gida don babu gado

Wani mutum mai suna Emmanuel Benson, wanda ya hadu da wasu mutane biyu da suka dawo daga Ingila a Legas, ya je yayi gwajin cutar COVID-19 kuma an tabbatar masa da yana dauke da ita.

Bayan kammala gwajin a asibitin koyarwa na jami'ar jihar Legas da ke Idi-Alaba ne aka ce ya koma gida don babu gadon kwantar da shi.

Benson wanda ya shirya tsaf don a killacesa sannan a bashi maganin muguwar cutar bayan ya gano yana dauke da ita a ranar 21 ga watan Maris, an bukaci ya koma gida don babu gadon kwantar dashi.

Jaridar SaharaReporters ta gano cewa bayan LUTH ta ki killace Benson, ya koma gida inda ya ci gaba da al'amuransa tare da shiga jama'a yadda ya saba.

"Daga LUTH din ya hau motar haya ne kuma ya ci gaba da mu'amala da jama'a yadda yake yi a baya," wani abokinsa ya sanar da jaridar SaharaReporters a ranar Alhamis.

Yadda LUTH suka ce mai cutar COVID-19 ya koma gida don babu gado
Yadda LUTH suka ce mai cutar COVID-19 ya koma gida don babu gado
Asali: Facebook

DUBA WANNAN: Bauchi: Majalisa ta shirya tsaf don tsige kakakinta

A lokacin da wakilin SaharaReporters ya tuntubesa a daren Alhamis din ta lambar wayarsa a manhajar WhatsApp, Benson ya tabbatar da cewa yana dauke da cutar kuma asibitin LUTH sun ki karbarsa.

Ya bayyana yadda ya je gwajin cutar bayan ya hadu da wasu da suka dawo daga Ingila a wata liyafar cin abincin dare a Legas a cikin makon da ya gabata.

Da aka tambayesa ko ya biya kudi wajen yin gwajin, Benson ya ki bayyana komai a kai. Ya ce baya son hankali ya dawo kansa don gudun jama'a su fara gudunsa.

A yayin hirar ne ya bayyana tsoronsa na idan ya sanar da jama'a yana dauke da cutar, za su dinga gudunsa. Tuni kuwa ya goge hoton da yasa a manhajar.

Ya ce, "A halin yanzu dai na killace kaina a gida. An yi min gwajin a LUTH ne duk da irin dogon layin da na samu. Wasu ma'aikatan lafiya ne suka shawarceni da in koma gida kuma in killace kaina na kwanaki 14 kuma za su dinga tuntubata don jin yadda lafiyata take,"

"Na samu cutar ne a wata liyafar cin abincin dare wacce wasu mutane biyu da suka dawo daga Ingila suka halarta. An yi min gwajin ne a ranar 21 ga watan Maris." Ya kara da cewa.

A lokacin da aka tambayesa ko yayi kokarin tuntubar NCDC don su san halin da ake ciki ko za su iya bashi taimakon, Benson ya ce, "Nayi ta kiran layikan NCDC din amma basu daukar wayata."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel