Majalisa ta fara rabon motocin alfarmar da ta sayo ma yan majalisun dokokin Najeriya

Majalisa ta fara rabon motocin alfarmar da ta sayo ma yan majalisun dokokin Najeriya

Majalisar wakilan Najeriya ta fara karbar motocin alfarma kirar Toyota Camry 2020 wanda ta yi odarsu domin amfanin yan majalisun, kuma tuni ta fara rabar da su ga yan majalisun da suka fi bukata.

Punch ta ruwaito ta hangi wasu daga cikin motocin ajiye a harabar majalisar, daga cikin motoci 400 da majalisar ta amince ta sayo bayan wani zama na musamman da ta gudanar a ranar 5 ga watan Feburairun shekarar 2020.

KU KARANTA: Majalisar wakilai ta bayar da kwangilar sayen motocin alfarma guda 400

Idan za’a tuna mun kawo muku rahoton cewa majalisar wakilai ta yi odan motocin alfarma guda 400 kirar Toyota Camry 2020 domin amfanin yan majalisar su 360, kamar yadda shuwagabannin majalisar suka yanke hukunci a wani taro da suka yi a ranar 5 ga watan Feburairu.

Jaridar Punch ta ruwaito wata majiya da ta nemi a sakaya sunanta ta tabbatar da amincewar majalisar na sayo motocin alarma guda 400, sai bata bayyana farashin da majalisar za ta sayo motocin a kai ba.

Majiyar Legit.ng ta tuntubi wakilin kamfanin motocin Elizade Nigeria Limited wanda yace har yanzu babu irin wannan motar a Najeriya, domin kuwa bata riga ta shigo ba, amma yace Toyoto Camry 2019 ta kai naira miliyan 26.75, yayin da V6 dinta ta kai N35.75m.

Sai dai wani bincike da majiyarmu ta yi a shafin yanar gizo na Toyota ya nuna motar Toyota Camry 2020 ta kai naira miliyan 9 zuwa naira miliyan 12.6, banda kudin daukota daga Japan zuwa Najeriya, wanda ya kai kashi 70 na kudin motar, da kuma sauran harajin da za’a biya musu wajen shigowa.

Su dai ire iren wadannan motoci da ake saya ma yan majalisa ana musu gwanjonsu ne a karshen zangon wa’adinsu arha raba-raba.

A wani labari kuma, A kokarinsa na hada kai domin ganin an ci galaba a kan annobar Coronavirus mai toshe numfashin dan Adam, shugaban kamfanin BUA, Abdul Samad Isiyaka Rabiu ya sanar da kyautar naira biliyan 1 ga gwamnatin tarayya.

Haka zalika, baya ga tallafin tsabar kudi N1,000,000,000 a yanzu haka Abdul Samad ya yi odan karin kayan asibiti da kuma hada da na’urori, injina da kayan gwajin cutar Coronavirus da za’a yi amfani dasu a jahohi guda 9.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel