COVID-19: Mu sadaukar da albashinmu na watan Maris - Dan majalisar wakilai

COVID-19: Mu sadaukar da albashinmu na watan Maris - Dan majalisar wakilai

- A yayin da Najeriya ke fuskantar babban kalubale sakamakon muguwar cutar coronavirus, 'yan majalisar tarayyar kasar nan sun fara wata shawara

- Dan majalisar tarayya Mansur Manu Soro, mai wakiltar mazabar Ganjuwa/Darazo ta jihar Bauchi, ya yi kira tare da mika bukata ga sauran 'yan majalisar

- Ya bukacesu da su hada naira miliyan dai-daya don siyan na'urorin taimakawa numfashi da kuma sauran kayayyakin asbiti da ake bukata

A yayin da Najeriya ke fuskantar babban kalubale sakamakon muguwar cutar coronavirus, 'yan majalisar tarayyar kasar nan na bukatar hadin kan junansu don hana tagayyarar talakan kasar nan.

Dan majalisar tarayya Mansur Manu Soro, mai wakiltar mazabar Ganjuwa/Darazo ta jihar Bauchi, ya yi kira tare da mika bukata ga sauran 'yan majalisar.

Ya bukacesu da su hada naira miliyan dai-daya don siyan na'urorin taimakawa numfashi da kuma sauran kayayyakin asbiti da ake bukata don yaki tare da amfanin masu fama da coronavirus.

A yayin zantawa da wakilin jaridar Daily Trust, Soro ya ce wannan gudumuwar za ta taimaka wajen siyan na'urorin taimakawa numfashi koda kuwa cutar tayi yawa a jikin mutum ta yadda baya iya numfashi da kyau.

COVID-19: Mu sadaukar da albashinmu na watan Maris - Dan majalisar wakilai
COVID-19: Mu sadaukar da albashinmu na watan Maris - Dan majalisar wakilai
Asali: Facebook

DUBA WANNAN: Buhari amince da fitar da N10bn don yaki da Coronavirus, ya umurci tsaffin ma'aikatan NCDC su koma aiki

Dan majalisar ya ce idan har abokan aikinsa suka bada naira miliyan daya kowannensu, toh za a hada naira miliyan 360. Ya ce kowanne na'urar taimakawa numfashi ana siyar da ita ne a kan naira miliyan tara da rabi.

"Shugabanci na bukatar sadaukarwa. Ina so in yi kira ga abokan aikin, 'yan majailsar wakilai, da mu sadaukar da albashinmu na watan Maris 2020 da kuma alawus dinmu don siyan na'urorin taimakawa numfashi," yace.

Ya kara da cewa, idan aka siya na'urorin, za a raba su ne a asibitocin gwamnatin jihohi 36 da birnin tarayya.

A bangarensa, dan majalisa Solomon Maren daga jam'iyyar PDP a jihar Filato, ya ce bukatar karfafa tattalin arziki na 2020 da aka mika ga majalisar tare da matakan, duk an yi su ne don 'yan Najeriya.

Ya ce bukatar duk an mika ta ne don ganin halin kalubalen tattalin arziki da cutar ta saka kasar nan.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel