Bauchi: Majalisa ta shirya tsaf don tsige kakakinta

Bauchi: Majalisa ta shirya tsaf don tsige kakakinta

A yayin da gwamnan jihar Bauchi ke killace bayan ya kamu da cutar Coronavirus, 'yan majalisar jihar 20 na jam'iyyar adawa ta APC a jihar ne suka kammala shirin tsige kakakin majalisar jihar, Abubakar Y. Suleiman, jaridar Leadership ta gano.

'Yan majalisar 20 na jam'iyyar APC din an gano masu biyayya ne ga tsohon Gwamna M.A Abubakar.

Jaridar Leadership ta gano cewa 'yan majalisar sun amince da tsige kakakin ne a kowanne lokaci na yinin yau Juma'a.

Majiya mai karfi daga majalisar jihar ta tabbatar wa da jaridar Leadership cewa sun fara yunkurin tsige kakakin ne tun ranar Asabar da ta gabata a yayin da suka halarci bikin diyar Alhaji Ali Kumo, na hannun daman tsohon gwamna M. A. Abubakar.

Tsohon gwamnan ya koka ga 'yan majalisar kan yadda gwamnatin Bala Mohammed ke shirin amfani da rahoton kwamitin samo dukiyar jihar da aka wawure don tozarta shi.

A don haka ne ya roki 'yan majalisar da su cece shi ta hanyar tsige kakakin majalisar wanda suka zarga da cika biyayya ga gwamna Bala Mohammed.

Bauchi: Majalisa ta shirya tsaf don tsige kakakinta
Bauchi: Majalisa ta shirya tsaf don tsige kakakinta
Asali: UGC

DUBA WANNAN: Buhari amince da fitar da N10bn don yaki da Coronavirus, ya umurci tsaffin ma'aikatan NCDC su koma aiki

'Yan majalisar da tsohon gwamnan tare da sauran shugabannin APC din da suka halarci taron a Gombe, sun zargi kakakin majalisar da hada kai da PDP da dukkan jami'anta, wanda suka ce bai dace ba.

Majiyar ta ce ana zargin kakakin majalisar da kin bin ra'ayin 'yan majalisar kwata-kwata.

An gano cewa 'yan majalisar sun amince da tsige kakakin ne bayan sun samu hadin kan dan majalisar jihar na jam'iyyar NNPP, Jamilu Umaru Dahiru, wanda hakan ya basu rinjayen biyu bisa kashi uku na 'yan majalisar.

Majiyar daga majalisar jihar ta ce, dan jam'iyyar NNPP din ya amince da bukatar 'yan majalisar APC din.

Wani dan majalisar jihar amma a karkashin jam'iyyar PDP wanda ya bukaci a boye sunansa, ya ce duk da 'yan jam'iyyar PDP din basu samun wata alfarma daga Gwamnan, amma za su kare Gwamnan da kakakin majalisar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel