Yanzu-yanzu: Gwamnatin jihar Legas ta mayar da filin kwallo asibitin jinyar masu Coronavirus

Yanzu-yanzu: Gwamnatin jihar Legas ta mayar da filin kwallo asibitin jinyar masu Coronavirus

Labarin da ke shigo mana da dumi-dumi na nuna cewa gwamnatin jihar Legas ta mayar da filin kwallon Mobolaji Johnson asibitin killace masu dauke da cutar Coronavirus a jihar.

Hotuna sun bayyana yadda ma'aikata ke aikin shirya gadaje da na'u'rori kuma ana kyautata zaton zasu kammlaa cikin kwana daya.

Zaku tuna cewa jihar Legas ce ke kan gaba wajen yawan masu dauke da cutar #COVID19 da mutane 30.

A yau, mun samu labarin cewa majinyata shida da ke fama da cutar coronavirus a jihar Legas ne a yau suka warke.

Za a sallamesu daga cibiyar killace majinyatan cutuka masu yaduwa da ke Yaba a jihar.

Tunde Ajayi, mai bada shawara ta musamman ga gwamnan jihar Legas, ya bayyana hakan a shafinsa na twitter a yau Alhamis.

Ya rubuta: "Shida daga cikin majinyatan cutar COVID-19 ne suka warke kuma za a sallamesu nan ba da daewa ba. Abinda jihar Legas ke yi a yanzu ya sha banban. Mu ne a gaba."

Yanzu-yanzu: Gwamnatin jihar Legas ta mayar da filin kwallo asibitin jinyar masu Coronavirus

asibitin jinyar masu Coronavirus
Source: Facebook

Yanzu-yanzu: Gwamnatin jihar Legas ta mayar da filin kwallo asibitin jinyar masu Coronavirus

filin kwallp

A wani labarin mai alaka, gwamnatin jihar Legas za ta samu tallafin N10 billion domin yakar Coronavirus.

Ministar kudi da kasafi, Zainab Ahmed, ta bayyana hakan ne inda sanar da yan majalisar cewa Najeriya ta samu tallafin $18.2 million daga hannun gwamnatin kasar Japan domin inganta cibiyoyin NCDC bakwai a fadin tarayya.

Hakazalika Gwamnatin tarayya za ta saki kudi N6.5 billion ga cibiyar takaita yaduwar cututttuka a Najeriya NCDC, ministar kudi, Zainab Ahmed Shamsuna, ta laburta.

Ta bayyana hakan a zaman ganawa da shugabannin majalisar dattawa a Abuja ranar Laraba.

Ministar ta bayyana cewa za'a saki kudin ne matsayin tallafi wajen yakar yaduwar cutar Coronavirus a Najeriya.

Zainab Ahmed, gwamnan CBN, da wasu masu ruwa da tsaki a bangare kudi sun gana da yan majalisar ne domin tattauna irin shirin da suke yi wajen rage burin kasafin kudin 2020 sakamakon illar da Coronavirus ta yiwa farashin danyen mai a kasuwar duniya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel