COVID-19: Buhari ba ya tari bayan gwaji, mu na zargin ma'aikatan Aso Rock 4,370 - Fadar shugaban kasa

COVID-19: Buhari ba ya tari bayan gwaji, mu na zargin ma'aikatan Aso Rock 4,370 - Fadar shugaban kasa

Gwamnatin tarayya ta ce tana kan tsamo mutanen da ake zargi da mu'amala da wadannda cutar COVID-19 ta kama. A halin yanzu kuwa ta tsamo mutane har 4,370.

Ta bayyana damuwarta da yadda da yawan wadanda suka dawo daga kasashen ketare suka bada adireshin bogi.

Gwamnatin tarayyar ta kara da cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari ba ya tari kuma an tabbatar da cewa baya dauke da muguwar cutar Coronavirus. Shugaban kasar na nan lafiya kalau kuma cikin koshin lafiya.

Ministan yada labarai da al'adu, Alhaji Lai Mohammed, ya sanar da hakan yayin bayani a game da cutar COVID-19.

Ya ce: "A halin yanzu mun zakulo mutane har 4,370 kuma muna rokon duk wanda yayi wata mu'amala da wadanda ke dauke da cutar ya garzaya ya kai kansa hukumomin da suka dace. Muna kira ga 'yan Najeriya da su goyi bayan hukumomin."

"Muna gab da bayyanar da cutar a tsakaninmu, don haka dole ne mu hana hakan ko kuma mu fuskanci kalubale mai yawa a kwanaki kadan masu zuwa. Babu wata hanya ne sai hakan."

Ministan ya ce gwamnati ta damu matuka ta yadda wasu masu dawowa daga kasashen ketare suka bada adireshin bogi.

COVID-19: Buhari ba ya tari bayan gwaji, mu na zargin ma'aikatan Aso Rock 4,370 - Fadar shugaban kasa
COVID-19: Buhari ba ya tari bayan gwaji, mu na zargin ma'aikatan Aso Rock 4,370 - Fadar shugaban kasa
Asali: UGC

DUBA WANNAN: Yanzu-yanzu: Mutane 6 da ke jinyar COVID-19 a Legas sun warke

"Babu boye-boye, zan iya cewa bama samun hadin kan da muke bukata a halin yanzu daga 'yan Najeriya. Wasu na nan suna caccakar gwamnati a maimakon hada kai da ita tare da bin ka'idojin hana yaduwar cutar.

"Wasu 'yan Najeriya da suka shigo kasar nan daga kasashen ketare sun bada adireshin bogi da lambar wayar karya. Hakan yasa muke fuskantar tsananin wahala wajen nemo su a lokacin da bukatar hakan ta taso.

"Wasu 'yan Najeeriya kuwa sun ki bin dokar rashin shiga jama'a masu yawa, yayin da wasu malaman addini suka ki bin dokar kasar.

"Gwamnati na yin duk abinda za ta iya amma muna bukatar hadin kan 'yan kasa. Mun wuce matakin roko da bayani, yanzu lokacin yin tilas ne."

A bangaren koshin lafiyar shugaban kasa Buhari, Ministan ya ce "Shugaban kasa na lafiya kuma cike da koshin lafiya. Hakazalika yana ci gaba da mulki. Wasu na zargin cewa shugaban kasar yana tari, wannan karya ne kuma labaran kanzon kurege ne marasa tushe da makama."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel