Abba Kyari: Wasu ‘Yan kwamitin PEAC sun killace kansu bayan taro a Abuja

Abba Kyari: Wasu ‘Yan kwamitin PEAC sun killace kansu bayan taro a Abuja

Wasu daga cikin ‘Yan majalisar PEAC da ke ba shugaban Najeriya shawara a kan harkar tattalin arziki sun dauki mataki na kare jama’a daga annobar cutar nan ta Coronavirus.

Yanzu haka wasu ‘Ya ‘yan wannan kwamiti sun rufe kansu a gida a sakamakon wata ganawa da su ka yi da shugaban kasa Muhammadu Buhari a fadar Aso Villa a Garin Abuja.

Jaridar Daily Trust ta bayyana cewa Farfesa Ode Ojuwu ya dauki matakin kare kansa, inda yanzu ya kebewa jama’a. Ode Ojuwu ya yi hakane bayan haduwarsa da Malam Abba Kyari.

A halin yanzu shugaban ma’aikatan fadar shugaban Najeriyar watau Abba Kyari ya na cikin wadanda aka tabbatar da cewa sun kamu da mummunar cutar nan ta Coronavirus.

Ganin cewa ya na cikin wadanda su ka hadu da Kyari ne Ode Ojuwu ya yi maza ya fara yin rigakafi, ya rufe kansa daga jama’a domin gudun yada cutar inda ya kamu da ita.

KU KARANTA: Coronavirus: Babu wanda ya kamu da COVI-19 a cikin ‘Yan Majalisar Tarayya

Abba Kyari: Wasu ‘Yan kwamitin PEAC sun killace kansu bayan taron farko a Abuja

‘Yan kwamitin PEAC sun hadu da Abba Kyari kafin a gano da ya na da cuta
Source: Facebook

Farfesa Ojuwu ya shaidawa Jaridar cewa bai da tabbacin ko dukkaninsu ‘yan kwamitin shugaban kasar sun hadu da Hadimin na Buhari, amma ya ce shi dai ya san ya kebe da shi.

“Ba zan ari bakin kowa in ci masa albasa ba. Ba ni da tabbacin cewa dukkanmu mun hadu da shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasar a Ranar Talata., 17 ga Watan Maris.”

Wannan Farfesa mai shekaru 72 a Duniya ya kara da cewa: “Ni dai na hadu da shi inda daga ni sai shi. Ina yi masa addu’ar samun waraka, ya cigaba da yi wa Najeriya hidima.”

A halin yanzu ‘Yan wannan kwamiti da Iyalansu ba su fita ko ina. Sauran ‘yan wannan majalisa sun hada da Dr. Shehu Yahaya, Dr. Iyabo Masha, da Farfesa Chukwuma Soludo.

Daga cikin ragowar wadanda Buhari ya nada domin su rika ba shi shawaran harkar tattalin arziki akwai: Dr. Bismark Rewane, Mohammed Adaya Salisu da kuma Doyin Salami.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit.ng

Online view pixel