Gwamnati ta rage kudin gangar mai, ta ware N6.5b domin yaki da COVID-19

Gwamnati ta rage kudin gangar mai, ta ware N6.5b domin yaki da COVID-19

A Ranar Laraba, 25 ga Watan Maris, 2020, gwamnatin tarayya ta sake duba lamarin kasafin kudin Najeriya na shekarar 2020, ganin yadda farashin danyen mai ya karye.

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa Ministar tattali da kasafin kudi, Zainab Ahmed, ta rage hasashen kudin da ta yi wa gangar danyen man Najeriya daga $57 zuwa $30.

Rahotanni sun ce Ministar ta bayyana wannan ne a lokacin da ta zauna da wasu shugabannin majalisar tarayyan kasar a tsakiyar makon nan a babban birnin tarayya Abuja.

A wannan taro na kusan sa’a hudu da aka yi, Misis Zainab Ahmed ta ce Najeriya ta na shiryawa duk wata matsalar tattalin arziki da za a iya fadawa a cikin wannan shekarar.

Shugaban majalisar dattawa, Sanata Ahmed Lawan, ya ce sun kira Ministar kasar ne domin ta yi wa majalisa bayani game da halin da kasafin kudin shekarar bana ya ke ciki.

Gwamnati ta rage kudin gangar mai, ta ware N6.5b domin yaki da COVID-19

Farashin mai ya karye a kasuwa zuwa $22 bayan barkewar COVID-19
Source: UGC

Haka zalika a wannan zama, shugabannin sun duba tsarin tattalin arzikin Najeriya na MTEF. Kasashe sun samu kansu cikin matsala ne bayan karyewar mai a kasuwa.

Bayan haka Ministar ta shugaba Buhari ta shaida cewa gwamnatin tarayya za ta fitar da kudi Naira biliyan 6.5 domin a yaki cutar Coronavirus ta addabi kasashen Duniya.

Ministar ta ce za a saki wadannan kudi ne ga hukumar NCDC mai kula da cututtuka a Najeriya. Gwamnati za ta fara fitar da Biliyan 1.5, sai kuma a saki Biliyan 5 daga baya.

Ahmed ta kuma fadawa ‘Yan majalisar tarayyar cewa Najeriya ta samu gudumuwar Dala miliyan 18.2 daga kasar Jafan domin bunkasa cibiyoyin NCDC da ke fadin kasar.

Daga cikin wadannan makudan kudi, gwamnatin Legas za ta samu tallafin Naira biliyan 10 daga hannun gwamnatin tarayya domin kawo karshen wannan cuta ta COVID-19.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit.ng

Online view pixel