COVID-19: An fara feshin magani a filin jirgin sama a Legas, za a yi wa sauran a Najeriya
- Hukumar kula da filayen jiragen sama na gwamnatin tarayya (FAAN) ta sanar da cewa ana feshin magani a filayen jiragen saman Najeriya
- Kamar yadda bidiyon ya bayyana, an fara feshin maganin kashe kwayoyin cuta a filin sauka da tashin jiragen sama na Murtala Muhammed da ke Legas
- Kamar yadda FAAN ta bayyana a shafinta na Twitter, za a yi feshin a sauran filayen jiragen saman kasar nan don gujewa yaduwar mugunyar cutar COVID-19
Hukumar kula da filayen jiragen sama na gwamnatin tarayya (FAAN) ta sanar da cewa ana feshin magani a filayen jiragen saman Najeriya.
Kamar yadda bidiyon ya bayyana, an fara feshin maganin kashe kwayoyin cuta a filin sauka da tashin jiragen sama na Murtala Muhammed da ke Legas.
Kamar yadda FAAN ta bayyana a shafinta na Twitter, za a yi feshin a sauran filayen jiragen saman kasar nan don gujewa yaduwar mugunyar cutar COVID-19.
KU KARANTA: Abinda ya hana Abba Kyari killace kansa bayan dawowa da kasar Jamus
A wani labari na daban, Abba Kyari, shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ki killace kansa bayan ya dawo daga kasar Jamus da Ingila ne saboda a lokacin da ya dawo ba a samu barkewar cutar coronavirus ba a kasashen, kamar yadda wata majiya daga iyalansa ta tabbatar.
Wannan kuwa ya ci karo da yadda jama’a ke yada cewa ya ki killace kansa ne duk da kuwa cibiyar kula da yaduwar cutuka ta kasa ta bada shawarar ya killace kansa din.
Na hannun daman shugaban kasar, a ranar Litinin an gano cewa yana dauke da muguwar cutar coronavirus wacce ake tsammanin ya samu ne a yayin da ya kai ziyara kasar Jamus.
“Abba Kyari ya ziyarci kasar Jamus da Ingila daga ranar 8 zuwa 12 ga watan Maris. Ya iso Abuja a ranar 13 ga watan Maris. A wannan lokacin kuwa, daga kasar Jamus zuwa Ingila duka babu barkewar cutar wacce za ta sa ya killace kansa,” wani daga cikin iyalansa ya sanar yayin da ya bukaci a rufe sunansa.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng