COVID-19: Ana feshin magani a kasuwannin jihar Kaduna
- Kasa da sa'o'i 24 bayan gwamnatin jihar Kaduna ta sanar da rufe kasuwanninta, hukumar habaka kasuwanni ta Kaduna ta fara feshin maganin kashe kwayoyin
- Duk da cewa ba a ji daga bakin babban manajan hukumar kula da habaka kasuwar ba, hukumar ta wallafa hakan a shafinta na Twitter inda take tabbatarwa
- Tun farko, 'yan kasuwa da ke tsakiyar birnin sun yi biyayya ga umarnin gwamnatin jihar inda suka zauna gida ba tare da sun bude shaguna ba
Kasa da sa'o'i 24 bayan gwamnatin jihar Kaduna ta sanar da rufe kasuwanni a jihar, hukumar habaka kasuwanni ta Kaduna ta fara feshin maganin kashe kwayoyin COVID-19 a kasuwannin.
An ga jami'a a kasuwar tunawa da Sheikh Abubakar Gumi suna feshi.
Duk da cewa ba a ji daga bakin babban manajan hukumar kula da habaka kasuwar ba, hukumar ta wallafa hakan a shafinta na Twitter inda take tabbatar da hakan.
Ta bayyana cewa, ana feshin ne don kashe duk kwayoyin cuta a kasuwar a matsayin hanyar yakar yaduwar cutar COVID-19.
Kamar yadda hukumar ta ce, "Da yammacin nan, ana feshin kasuwar Sheikh Abubakar Gumi don kashe kwayoyin cuta tare da hana yaduwar muguwar cutar COVID-19."
Tun farko, 'yan kasuwa da ke tsakiyar birnin sun yi biyayya ga umarnin gwamnatin jihar inda suka zauna gida ba tare da sun bude shaguna ba.
KU KARANTA: Yanzu-yanzu: Abba Kyari ya isa asibitin Gwagwalada don fara magance cutar COVID-19
A kasuwar Gumi da ta Kakuri da ke kananan hukumomin Kaduna ta Arewa da Kaduna ta Kudu, shaguna da yawa suna rufe yayin da masu siyar da magunguna, danyen abinci, dafaffen abinci, kayan sha da sauransu duk suna ci gaba da al'amuransu.
Amma kuma, an ga jama'a suna ta tururuwar siyen kayan abinci don tunanin ko za a rufe jihar Kaduna baki dayanta a kan cutar.
An ga jama'a da takunkumin fuska inda wasu ke tafe da sinadarin kashe kwayoyin cuta na hannu, yayin da wasu basu damu ba.
Hakazalika, an ga tarin jama'a suna layi wajen cikar tukunyar gas, bankuna da kuma cika tankunan motocinsu da man fetur.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng