Bayan gwajin cutar COVID-19, Shugaba Buhari ya koma ofis a Abuja

Bayan gwajin cutar COVID-19, Shugaba Buhari ya koma ofis a Abuja

Wata Majiya daga fadar shugaban kasa ta bayyana cewa shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya koma bakin aiki a Ranar Laraba, 25 ga Watan Maris, 2020.

Kamar yadda Majiyar ta shaidawa Jaridar Daily Trust, shugaban kasar ya yi aiki a ofishinsa har zuwa karfe 2:30 na rana, a daidai lokacin da ake fama da annoba.

Rahotanni sun bayyana cewa babu wani jami’in wata hukuma ko kusa a gwamnati da ya gana da shugaban kasar domin yi masa bayanai kamar yadda aka saba.

A jiya Laraba, ya kamata ace an gudanar da taron FEC, sai dai an dakatar da duk wani irin wannan zama kamar yadda kwamitin nan na PTFCOVID ta bada shawara.

Haka zalika shugaban kasar ya amince da dakatar da babban taron shugabannin kasa wanda aka shirya za ayi a yau, duk don a kare yaduwar wannan Coronavirus.

KU KARANTA: Masu dauke da cutar COVID-19 a Najeriya sun karu - NCDC

Bayan gwajin cutar COVID-19, Shugaba Buhari ya koma ofis a Abuja

Buhari ya koma ofis bayan gwaji ya nuna bai da cutar COVID-19
Source: Facebook

A cikin makon nan ne aka samu labari cewa shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa watau Malam Abba Kyari da wasu ma’aikatansa sun kamu da cutar COVID-19.

Hakan ya na nufin shugaba Muhammadu Buhari ya na aiki ne ba tare da babban Hadiminsa Abba Kyari ba, wanda ya ke tsara yadda abubuwa su ke gudana a cikin Aso Villa.

A dalilin haka ne gwamnatin tarayya ta takaita hada-hadar da ake yi a fadar shugaban kasa, duk wannan ya na cikin matakan dakile yaduwar cutar da ta barke a kasashe.

Rahotannin da mu ka samu sun bayyana cewa jami’an tsaro na DSS ba su barin mutane fiye da 50 su shiga cikin fadar shugaban kasa a lokaci domin kare lafiyar jama’a.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit.ng

Online view pixel