Yanzun nan: An sanar da sakamakon gwajin Coronavirus da aka yi ma gwamnan Nassarawa
Fadar gwamnatin jahar Nassarawa ta fitara da sanarwa game da sakamakon gwajin da jami’an hukumar kiyaye yaduwar cututtuka ta Najeriya, NCDC ta gudanar a kan gwamnan jahar, Abdullahi Sule.
Legit.ng ta ruwaito sanarwar ta tabbatar ma al’ummar jahar Nassarawa, yan uwa da abokan arzikin gwamnan da ma sauran jama’an Najeriya cewa gwamnan ya sha, duba da cewa sakamakon gwajin ya nuna baya dauke da kwayar cutar Coronavirus mai toshe numfashi.
KU KARANTA: Jerin manyan mutanen da suka yi cudanya da Abba Kyari kafin a tabbatar ya kamu da Coronavirus
Sai dai duk da wannan tabbaci da sakamakon gwajin ya nuna, Gwamna
Abdullahi Sule ya dauki matain killace kansa tare da cigaba da gudanar da aiki daga gida domin ya rage cudanya da jama’a, don gudun kada kuma ya kamu.
Sanarwar ta kara da cewa: “Idan za’a tuna, Gwamna Sule da kansa ya gayyaci jami’an NCDC zuwa fadar gwamnatin jahar domin su gudanar da gwajin cutar a kansa, amma dukkanin gwaje gwajen da aka gudanar sun nuna baya dauke da ita.
“Za’a cigaba da sanar da jama’a duk wani cigaba da aka samu game da matsayin lafiyar mai girma Gwamna Abdullahi Sule.”
A hannu guda,gwamnatin jahar Nassarawa ta tabbatar sa samun wani mutumi da ke tunanin yana dauke da kwayar cutar Coronavirus a tattare da shi, a asibitin kwararru dake Lafia.
Kwamishinan kiwon lafiya na jahar ya bayyana cewa mutumin ya shiga jahar Nassarawa ne daga babban birnin tarayya Abuja don halartar daurin aure a unguwar Arikya dake garin Lafiya, a lokacin aka gano alamun cutar.
“Da gaske ne mun samu rahoton samun wani da ake zargi yana dauke da Coronavirus, da misalin karfe 5 na yamma, daga Abuja ya shigo, amma a yanzu jami’anmu sun killace shi, mun fara bin diddigin mutanen da ya yi mu’amala dasu.” Inji kwamishina Baba Yahaya.
A wani labarin kuma, karamar ministar babban birnin tarayya Abuja, Ramatu Aliyu ta bayyana cewa ta hukumar yaki da yaduwar cututtuka a Najeriya ta gudanar da gwajin annobar nan mai toshe numfashin dan Adam, watau Coronavirus a kanta.
Ramatu ta bayyana cewa ta yi mu’amala da mutanen da gwaji ya tabbatar da cewa suna dauke da cutar, hakan ne yasa wajibi ita ma ta yi wannan gwaji domin sanin matsayinta.
Zuwa yanzu dai hukumar yaki da yaduwar cututtuka ta Najeriya, NCDC ta bayyana cewa daga cikin mutane 46 da aka samu suna dauke da cutar Corona, mutane 8 a babban birnin tarayya Abuja su ke, daga cikinsu har da shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa, Abba Kyari.
Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa
ko a http://twitter.com/legitnghausa
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com
Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa
Asali: Legit.ng