Ana wata ga wata: An yi garkuwa da Yayan gwamnan Bauchi kwana daya da kamuwarsa da Corona

Ana wata ga wata: An yi garkuwa da Yayan gwamnan Bauchi kwana daya da kamuwarsa da Corona

Wannan shi ne rana zafi inuwa kuna, ba’a gama jimamin kamuwar gwamnan Bauchi, Bala Muhammad da annobar Coronavirus ba, kwatsam sai ga wasu gungun miyagu yan bindiga sun sace Yayansa, Yaya Adamu.

Jaridar Punch ta ruwaito yan bindiga sun yi awon gaba da Yaya Adamu ne a ranar Laraba, 25 g watan Maris da misalin karfe 7:30 na dare a gidansa dake Unguwan Jaki, cikin kwaryar garin Bauchi.

KU KARANTA: Jugum jugum: Ministar Abuja na zaman jiran fitowar sakamakon gwajin Coronavirus

Wannan lamari ya faru ne bayan kimanin sa’o’i 72 da gwamnan jahar Bauchi, Bala Muhammad ya killace kansa daga cudanya da jama’a sakamakon mu’amalar da ya yi da wani mutumi dake dauke da cutar Coronavirus.

Daga bisani a ranar Talata aka tabbatar da gwamnan ya kamu da cutar, bayan sakamakon gwajin da jami’an hukumar kiyaye yaduwar cututtuka ta kasa, NCDC, suka gudanar a kansa ya tabbatar da hakan.

Babban hadimin gwamnan a kan harkokin watsa labaru, Mukhtar Gidado ne ya tabbatar da aukuwar lamarin ga majiyar Legit.ng ta misalin karfe 9:30 yayin wata hirar tarho da ta yi da shi.

A wani labarin kuma, Labarin mai inganci daga wakilinmu dake jihar Bauchi na nuna cewa gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed Kauran Bauchi, ya kamu da cutar Coronavirus.

A wani jawabin da mai magana da yawun gwamnan, Muhktar M Gidado ya saki, ya tabbatar da rahoton inda ya bukaci alumma su taimakawa gwamnan da addu'o'i. Jawabin yace:

“Muna sanar da daukacin jama’a cewa sakamakon gwajin mutane shida da cibiyar takaita yaduwar cututtuka ta gudanar kan gwamna Bala AbdulKadir Mohammed, iyalansa, da hadimansa da suka raka sa Legas ya fito.

“Daga cikin sakamakon shida na mutum daya kadai ya tabbata ya kamu, kuma shine na Sanata Bala AbdulKadir Mohammed, gwamnan jihar Bauchi.“ “A yanzu haka, gwamnan ya killace kansa yayinda likitoci da maaiktakan hukumar sun dauki nauyin kula da shi’.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel