Coronavirus: Sakamakon gwajin Ali Nuhu, Maishadda, Ado Gwanja ya fito

Coronavirus: Sakamakon gwajin Ali Nuhu, Maishadda, Ado Gwanja ya fito

Sakamakon gwajin cutar COVID19 da shahrarren dan wasan kwaikwayon Kannywood da Nollywood, Ali Muhammad Nuhu, tare da Frodusa, Abubakar Bashir Maishadda, Dirakta Hassan Giggs da mawaki Ado Gwanja, ya fito.

A cewar Maishadda, dukkansu basu kamu da cutar kuma suna mika godiya ga masoya bisa addu'o'insu.

Za ku tuna cewa Ali Nuhu da wasu jaruman Kannywood sun halarci taron lambar yabon AMVCA a Legas inda kwamishanan kiwon lafiyan Legas, Farfesa Abayomi, ya bukaci dukkan wadanda suka halarci taron su gwada kansu saboda akwai yiwuwan sun kamu da Coronavirus.

Maishadda yace “Kowa zai iya kiran kansa abokinka amma baka sanin abokin kwarai sai lokacin kunci. Mun godewa addu'o'inku. Muna cikin koshin lafiya.“

Coronavirus: Sakamakon gwajin Ali Nuhu, Maishadda, Ado Gwanja ya fito
Coronavirus: Sakamakon gwajin Ali Nuhu, Maishadda, Ado Gwanja ya fito
Asali: Facebook

KU KARANTA Kakakin majalisar dokokin jihar Edi ya kamu da Coronavirus

A bangare guda, Ministan babbar birnin tarayya, Muhammad Musa Bello, ya ce za a mayar a babbar asibitin Zuba zuwa cibiyar killace mutane duk a matakan da ake dauka na hana yaduwar cutar coronavirus a Abuja.

Da yake jawabi ga manema labarai, Bello ya ce yana aiki tare da asibitin koyarwa na jami’ar Abuja domin bunkasa cibiyar killace masu dauke da cutar na Gwagwalada.

Ya jadadda cewar har yanzu akwai dokar hana taron jama’a da suka tasar ma mutane 50; yayinda ya kaddamar da rufe harkoki kadan a birnin tarayyar.

Ya umurci ma’aikatan gwamnati daga matsayi na 12 zuwa kasa da su fara zaman gida daga jiya Talata, yayinda wadanda suka kasanceyan gaba a harkoki za su ci gaba da zuwa aiki.

Ministan ya bukaci mazauna yankin da su kwantar da hankulansu kada su sanya tsoro a rai domin kasuwanni za su ci gaba da budewa domin siyar da abinci da sauran kayayyakin bukata.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel