Maracana zai zama wajen kula da Marasa lafiya saboda Coronavirus

Maracana zai zama wajen kula da Marasa lafiya saboda Coronavirus

Mun samu labari cewa Maracana na kasar Brazil wanda ya na cikin manyen filayen wasannin Duniya ya zama dakin kula da masu dauke da cutar Coronavirus ta COVID-19.

Gidan talabijin na CNN ta bayyana cewa an koma jinyar wadanda su ka kamu da cutar a filin wasan na Maracana da ke Birnin Rio de Janiero mai cin akalla mutane 78, 000.

Filin wasan da aka yi amfani da shi wajen Gasar kwallon kafan Duniya a shekarar 2014, a wancan lokaci an kashe masa makudan kudi, daga baya ya sake tabarbarewa.

A makon da ya gabata ne hukumar kwallon kafa na kasar ta dakatar da duk wasu harkar wasanni. An dauki wannan mataki ne saboda barkewar annobar Coronavirus a kasar.

KU KARANTA: COVID-19: Ronaldo da Mendes za su bada gudumuwar gadajen asibiti

Bayan filin Maracana, ana tunanin gwamnatin za ta rufe katafaren filin wasan nan na Pacaembu domin ajiye masu larurar Coronavirus har zuwa lokacin da su ka samu sauki.

Hukumomin Brazil sun dauki wannan mataki ne bayan ‘Yan wasa sun fara yin zanga-zanga bayan rahotanni sun bayyana cewa sama da mutane 1000 sun kamu da cutar.

An gina wannan filin wasa ne tun a shekarar 1950 lokacin da aka buga gasar kwallon cin kofin Duniya. A wannan filin wasa ne ‘Dan wasan Kasar Brazil Pele ya yi tashensa.

A Garin Sao Paulo, inda cutar Coronavirus ta yi kamari, hukumomi sun bayyana cewa za a kara gadajen jinya 2000 a cikin ‘yan kwanakin nan masu zuwa saboda wannan cuta.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng