COVID-19: Gwamnan Bayelsa ya musanta haduwarsa da Kyari ko Mohammed
- Gwamnan jihar Bayelsa, Sanata Douye Diri, ya musanta haduwa da Abba Kyari, shugaban ma’aikatan fadar Muhammadu Buhari
- Diri ya sanar da hakan ne yayin da ya ziyarci cibiyar killace masu cuta mai yaduwa a asibitin koyarwa na Niger Delta da ke Okolobiri
- Ya ce gwamnatin jihar na kokarin daukar matakai don tabbatar da cewa kwayar cutar ba ta ci gaba da yaduwa ba a jihar
Gwamnan jihar Bayelsa, Sanata Douye Diri, ya musanta haduwa da Abba Kyari, shugaban ma’aikatan fadar Muhammadu, kafin a tabbatar yana dauke da muguwar cutar coronavirus.
Diri ya sanar da hakan ne yayin da ya ziyarci cibiyar killace masu cuta mai yaduwa a asibitin koyarwa na Niger Delta da ke Okolobiri, a karamar hukumar Yenagoa ta jihar a ranar Laraba.
Ya bayyana cewa, a lokacin da ya hadu da gwamnan jihar Bauchi yayin taron hukumar tattalin arziki ta kasa, tsohon ministan FCT din bai samu cutar ba.
Diri, wanda ke yin martani a kan kiran da ‘yan jihar Bayelsa ke yi garesa a kan cewa ga killace kansa bayan zama tare da gwamnan jihar Bauchi, ya ce ba haka bane.
DUBA WANNAN: COVID-19: Jirgin sama daga Turai yana tunkaro Legas duk doka ta hana
Ya ce gwamnatin jihar na kokarin daukar matakai don tabbatar da cewa kwayar cutar ba ta ci gaba da yaduwa ba a jihar.
Ya bayyana cewa tuni asbitin ya fara samar da sinadarin kashe kwayoyin cutuka na hannu, takunkumin fuska da kuma sauran kayayyakin kariya daga cutar.
Yace gwamnatin jihar ta dau matakan kariya ga iyakokinta na ruwa da tudun don tantance bakin da ke shigowa jihar.
Yace: “Ban samu wata haduwar jiki da Gwamna Bala Muhammed da Abba Kyari ba. Ko a taron, mun zauna ne a tsare. Ko a taron NEC din, mun zauna kusa da juna amma a lokacin bai samu ciwon ba. A lokacin taron kuwa, Abba Kyari baya nan don an sanar damu cewa yana kasar Jamus. Hakan kuwa yasa na dinga mamakin yadda aka yi har ake yada cewa na hadu da shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasan.”
“A bangaren Bala Muhammed kuwa, tabbas mun zauna kusa da juna a taron NEC din, amma a lokacin bashi da cutar,” yace.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng