Toyin Saraki ta tattaro Masana daga Landan zuwa Najeriya a kan annobar Coronavirus

Toyin Saraki ta tattaro Masana daga Landan zuwa Najeriya a kan annobar Coronavirus

Uwargidar tsohon shugaban majalisar dattawa Bukola Saraki watau Toyin Saraki, ta dauki mataki na ganin bayan annobar Coronavirus da ta barke a kasashe da-dama.

Dr. Toyin Saraki ta bayyana cewa ta hada-kan wasu kwararrun Likitoci da Malaman kiwon lafiya da za su taimaka wajen rage yaduwar wannan muguwar cuta a Najeriya.

Toyin Saraki ta bayyana wannan ne ta bakin Mai magana da yawun bakinta, Shola Ayelabola, kamar yadda mu ka samu labari daga Jaridar Daily Trust a makon nan.

A cewar Dr. Toyin Saraki, ya kamata ta ba kasar ta Najeriya gudumuwarta a matsayinta ta babbar Jami’ar hukumar lafiya ta Duniya watau WHO a Yankin Nahiyar Afrika.

Matar tsohon gwamnan Kwara ta yi wannan jawabi ne a Ranar Talata, 24 ga Watan Maris. Saraki ta nuna cewa akwai bukatar ta sa hannu wajen maganin wannan annoba.

KU KARANTA: Ronaldo ya na kokarin ceton rayukan wadanda su ka kamu da COVID-19

Toyin Saraki ta tattaro Masana daga Landan zuwa Najeriya a kan annobar Coronavirus
Ainihi Toyin Saraki Malamar asibiti ce kamar Mai gidanta Bukola Saraki
Asali: Facebook

Likitar ta bayyana cewa kungiyarta, za ta hada-kai da Wendy Graham wanda babban Farfesan lafiya ne a wata makarantar koyon aikin asibiti da ke Landan a Ingila.

“A wajen yaki da cutar Coronavirus, dole mu yi amfani da ilminmu wajen yin abin da ya dace, tsabtace hannuwa da kuma sauran wuraren da ake tabawa.” Inji Saraki.

Wannan Baiwar Allah ce ta ke shugabantar shirin nan na Wellbeing Foundation Africa wanda ta kafa domin taimakawa sha’anin kiwon lafiya a kasashen Nahiyar Afrika.

Farfesa Wendy Graham da Tawagarsa, za su taimakawa Najeriya wajen rage yaduwar wannan cuta ta COVID-19. Yanzu akalla mutum 40 sun kamu da cutar a kasar.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng