Coronavirus: Atiku Abubakar ya yi wa Abba Kyari addu’ar samun lafiya

Coronavirus: Atiku Abubakar ya yi wa Abba Kyari addu’ar samun lafiya

Tsohon mataimakin shugaban Najeriya, Alhaji Atiku Abubakar, ya yi magana bayan labari ya zo masa cewa Hadimin shugaban kasa, Abba Kyari ya kamu da COVID-19.

Kamar yadda mu ka ji, Atiku Abubakar ya aika gajerar addu’a mai muhimmanci a daidai wannan lokaci ga Malam Abba Kyari wanda aka gano ya na dauke da Coronavirus.

Atiku Abubakar ya yi magana ne bayan Jaridar This Day ta rahoto cewa an gano shugaban ma’aikatar fadan Najeriya ya kamu da wannan mummunar cuta ta COVID-19.

An fara rade-radin Kyari ya kamu da cutar ne tun a Ranar Litinin. Sai a jiya Talata ne aka samu tabbacin cewa gwajin da aka yi ya nuna Hadimin shugaban kasar ya kamu.

Wazirin Adamawa, Atiku Abubakar ya ajiye siyasa a gefe guda, ya rokawa Hadimin shugaban kasa Buhari addu’ar samun sauki daga wannan cuta da ta zama a annoba a yau.

KU KARANTA: Tsoron kamuwa da COVDI-19 ta sa wani Gwamna ya rufe kansa a daki

Da ya ke magana a shafinsa na Tuwita, Atiku ya ce: Tunanin Shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa, Abba Kyari, ya na cikin ranmu, kuma ya na cikin addu’o’inmu.”

‘Dan takarar shugaban kasar a zaben 2019, ya kuma kara bayani da harshen Hausa inda ya ce: “Allah ya karemu baki daya." A karshe ya roka masa samun lafiyar Ubangiji.

Alhaji Atiku ya aika wannan sako ne da kimanin karfe 10:00 na safiyar jiya Ranar Laraba, jim kadan bayan wannan labari maras dadi ya fara karada gidajen jaridu a Najeriya.

Kafin nan Uwargidar shugaban kasa Buhari, Aisha Buhari ta yi irin wadannan addu’o’i bayan ta samu labarin cewa Yaron Atiku Abubakar ya kamu da wannan cuta ta COVID-19.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit

Online view pixel