Ministan Abuja zai mayar da abitin Zuba cibiyar killace masu coronavirus

Ministan Abuja zai mayar da abitin Zuba cibiyar killace masu coronavirus

- Ministan babbar birnin tarayya, Muhammad Musa Bello, ya ce za a mayar a babbar asibitin Zuba zuwa cibiyar killace mutane masu coronavirus

- Hakan na daga cikin matakan da ake dauka na hana yaduwar cutar coronavirus a Abuja

- Ya jadadda cewar har yanzu akwai dokar hana taron jama’a da suka tasar ma mutane 50

Ministan babbar birnin tarayya, Muhammad Musa Bello, ya ce za a mayar a babbar asibitin Zuba zuwa cibiyar killace mutane duk a matakan da ake dauka na hana yaduwar cutar coronavirus a Abuja.

Da yake jawabi ga manema labarai, Bello ya ce yana aiki tare da asibitin koyarwa na jami’ar Abuja domin bunkasa cibiyar killace masu dauke da cutar na Gwagwalada.

Ya jadadda cewar har yanzu akwai dokar hana taron jama’a da suka tasar ma mutane 50; yayinda ya kaddamar da rufe harkoki kadan a birnin tarayyar.

Ministan Abuja zai mayar da abitin Zuba cibiyar killace masu coronavirus
Ministan Abuja zai mayar da abitin Zuba cibiyar killace masu coronavirus
Asali: Facebook

Ya umurci ma’aikatan gwamnati daga matsayi na 12 zuwa kasa da su fara zaman gida daga jiya Talata, yayinda wadanda suka kasanceyan gaba a harkoki za su ci gaba da zuwa aiki.

Ministan ya bukaci mazauna yankin da su kwantar da hankulansu kada su sanya tsoro a rai domin kasuwanni za su ci gaba da budewa domin siyar da abinci da sauran kayayyakin bukata.

Kwamishinan yan sanda na birnin tarayya, Bala Ciroma, ya ce hukumar, tare da hadin gwiwar sauran hukumomin tsaro, sun zuba jami’ai domin tabbatar da bin doka na hana taro.

KU KARANTA KUMA: Coronavirus: Likita dan shekara 26 ya mutu bayan ya sadaukar da lokaci yana taimakon wadanda suka kamu

Darakar cibiyar kira na birnin tarayya, Jumai Ahmadu, ta bukaci mazauna yankin da su kai rahoton kowani coci, masallaci, wajen rawa, wurin kallo da sauran wuraren taro da suka saba umurnin ta lambobin waya kamar haka; 08099936314, 08099936313.

A wani labarin mun ji cewa biyo bayan halartan taron kungiyar gwamnonin Najeriya da na tattalin arziki na kasa, Gwamna Godwin Obaseki ya shiga killace kansa.

A wani jawabi da aka saki a ranar Laraba, 25 ga watan Maris daga hadimin Obaseki, Crusoe Osagie, ya bayyana cewa Gwamna Bala Mohammed na Bauchi da Abba Kyari, Shugaban ma’aikatan Shugaban kasa Muhammadu Buhari, wadanda ke dauke da cutar coronavirus duk sun halarci taron.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng