Coronavirus: ‘Dan wasan Juventus Ronaldo zai saye kayan asibiti a kasar Portugal

Coronavirus: ‘Dan wasan Juventus Ronaldo zai saye kayan asibiti a kasar Portugal

Mun ji labari cewa fitaccen ‘Dan wasan kwallon kafa, Cristiano Ronaldo, ya koma gida inda ya ke kokarin taimakawa Bayin Allah da su ka kamu da cutar nan ta Coronavirus.

Cristiano Ronaldo mai shekaru 35 zai bada gudumuwar kudi ga wasu asibitocin kasar Portugal domin ganin an shawo karshen cutar COVID-19 da addabi Duniya a halin yanzu.

‘Dan wasan gaban na Juventus da kuma Attajirin Dillalinsa watai Jorge Mendes ne su ka hada-kai, su ka ba babban nasibitin koyar da aikin Likitanci na Arewacin Lisbon gudumuwa.

Haka zalika wadannan Bayin Allah sun bada irin wannan taimako ga asibitin Porto's Santo Antonio da ke babban birnin Portugal kamar yadda mu ka samu labari daga tashar ESPN.

Yanzu za a radawa sashen dakunan kula da masu mummunan rashin lafiya sunayen Cristiano Ronaldo da Jorge Mendes, saboda irin wannan abin a yaba da su ka yi wa kasar ta su.

KU KARANTA: Kocin Arsenal da ya kamu da cutar Coronavirus ya murmure

Ronaldo da Mendes za su bada kudin da za a gyara wadannan sashe na asibitocin, inda za a cika su da duk kayan aikin da ake bukata domin kula da wadanda cutarsu ta yi kamari.

A kowane sashe za a zuba gadaje goma kamar yadda tashar ESPN ta shaida. Cristiano Ronaldo da Mendes ne za su dauki wannan nauyi ba tare da sisin kobo daga hannun kowa ba.

“Za a zuba gadajen jinya, na’urar taimakawa numfashi, na’urar lura da bugun zuciya, da allurori da sauran muhimman kayan aikin da masu fama da cutar COVID-19 su ke bukata.”

Kwanakin baya aka rika yada rade-radin cewa Ronaldo ya maida wani otel dinsa wajen kula da wadanda su ka kamu da cutar Coronavirus, mun gano hakan ba gaskiya ba ne.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit

Online view pixel