Ni ban gaisa da Gwamna Bala Mohammed ba – Inji Mohammed Atiku Abubakar

Ni ban gaisa da Gwamna Bala Mohammed ba – Inji Mohammed Atiku Abubakar

Mai girma gwamnan Bauchi, Sanata Bala Abdulkadir Mohammed ya na cikin wadanda aka tabbatar cewa sun kamu da cutar nan ta Coronavirus a Najeriya.

Wani daga cikin Hadiman Gwamnan, Mukhtar Gidado, ya fito ya bayyana cewa Mai gidan na sa ya kamu da cutar ne bayan ya hadu da Mohammed Atiku Abubakar.

Mukhtar Gidado ya fitar da jawabi jiya ya na cewa Bala Abdulkadir Mohammed ya gaisa da ‘Dan tsohon mataimakin shugaban kasar, har kuma sun yi musafaha.

Sai dai kuma yanzu rahotanni sun zo mana cewa Alhaji Mohammed Atiku Abubakar, ya karyata wannan jawabi da ya fito daga gidan gwamnatin na jihar Bauchi.

Yaron tsohon mataimakin shugaban Najeriyar ya musanya zargin cewa ya mikawa Gwamnan hannu, a cewarsa gaisawa kurum su ka yi ba tare da musafaha ba.

KU KARANTA: COVID-19: An fito da gwajin wadanda aka killace a Garin Kaduna

Ni ban gaisa da Gwamna Bala Mohammed ba – Inji Mohammed Atiku Abubakar
Yaron Atiku ya ce bai ba Gwamna Bala Mohammed hannu ba
Asali: Getty Images

Atiku Abubakar ya bayyana wannan ne a wani sako da ya aikawa gidan Jaridar Premium Times, bayan Manema labarai sun bukaci jin ta bakinsa game da lamarin.

Matashin wanda yanzu ya kil killace a asibiti a Abuja ya ce: “Mun gaisa, amma ba mu sha hannu ba.” Rahotannin sun ce ya bayyana wannan ne ta kafar WhatsApp.

Maras lafiyan ya nuna cewa sun zaune ne tare da Iyalansu a gefe daban-daban na jirgin saman da ya dauko su tare da Tawagar gwamnan daga Legas zuwa Abuja.

Sai dai Jaridar Premium Times ta zurfafa bincike inda ta gano cewa Bala Mohammed ya yi tafiya zuwa kasar waje, hakan na nufin akwai yiwuwar a can ya dauko cutar.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel