Masu dauke da coronavirus yanzu a Najeriya sun kai 46 yayinda NCDC ta tabbatar da sabbin mutane 2

Masu dauke da coronavirus yanzu a Najeriya sun kai 46 yayinda NCDC ta tabbatar da sabbin mutane 2

- Yanzu mutane da ke dauke da coronavirus a Najeriya sun kai 46 bayan an sake samun sabbin mutane biyu

- Cibiyar kula da cututtuka ta Najeriya ce ta sanar da hakan a safiyar yau, Laraba, 25 ga watan Maris

- An samu mutum guda a jahar Osun yayinda dayan ke a jahar Lagas

Cibiyar kula da cututtuka ta Najeriya (NCDC) ta bayyana cewa an samu Karin mutane biyu da ke dauke da cutar coronavirus a Najeriya.

Hukumar NCDC ta shafinta na Twitter a ranar Talata, 24 ga watan Maris, ta bayyana mutum guda a Osun yayinda dayan ya ke a jahar Lagas.

Masu dauke da coronavirus yanzu a Najeriya sun kai 46 yayinda NCDC ta tabbatar da sabbin mutane 2

Masu dauke da coronavirus yanzu a Najeriya sun kai 46 yayinda NCDC ta tabbatar da sabbin mutane 2
Source: Twitter

Ta wallafa: “An tabbatar da sabbin lamuran #COVID19 a Najeriya: 1 a Lagas sannan 1 a Osun.

“Dukaninsu sun kasance matafiya da suka dawo Najeriya cikin kwanaki 7 da suka gabata.

“Da misalin karfe 07:00 na safiyar ranar 25 ga watan Maris, an tabbatar da masu dauke da #COVID19 46 a Najeriya. An sallami mutane 2 sannan mutum 1 ya mutu.”

A bangare guda mun ji cewa Bala Mohammed, gwamnan jihar Bauchi, ya bukaci jama'ar jiharsa da kada su ji tsoro a kan kebancesa da aka yi sakamakon cutar coronavirus da ya kamu da ita.

A ranar Talata ne dai aka tabbatar da cewa gwamnan na dauke da cutar coronavirus din.

Mohammed ya killace kansa tun bayan da yayi hannu da dan Atiku Abubakar, tsohon mataimakin shugaban kasar Najeriya, wanda aka gano yana dauke da cutar, kamar yadda jaridar The Cable ta wallafa.

KU KARANTA KUMA: Coronavirus: Gwamnatin Kano ta hana manyan motocin daukar fasinjoji shiga jahar

A sakon da gwamnan ya wallafa a shafinsa na twitter, Mohammed ya ce yana lafiya kuma har yanzu bai fara nuna wata alama ta cutar ba.

"Kamar yadda zai yuwu kun sani, an gano ina dauke da coronavirus," Mohammed yace.

"Tuni na killace kaina na kwanakin da suka gabata kuma har yanzu ina kebance har sai na samu tabbaci daga likitoci cewa zan iya ci gaba da mu'amala da jama'a. Ina lafiya kuma ban fara nuna wata alamar cutar ba. Ina kira ga kowa da ya kwantar da hankali kuma kada a firgita. Za mu tsallake." yace.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel