Coronavirus: Gwamnan APC ya zabtare rabin alawus din 'yan siyasar jiharsa

Coronavirus: Gwamnan APC ya zabtare rabin alawus din 'yan siyasar jiharsa

- Gwamnan jihar Filato ya zabtare alawus din masu rike da mukaman siyasa a jihar sakamakon barkewar annobar coronavirus

- Kamar yadda gwamnan yace, za a zabtare alawus din masu mukaman siyasa din da kashi 50 wato rabi kenan

- A dukkan fadin duniya, gwamnatoci na daukar matakan masu tsauri don samun mafita a yayin wannan annobar

Gwamnan jihar Filato, Simon Lalong ya zabtare alawus din masu mukaman siyasa a jihar a yayin da cutar coronavirus ta barke a Najeriya.

Lalong ya bayyana hakan ne a ranar Talata, 24 ga watan Maris a yayin zantawa da manema labarai tare da jawabi ga mazauna jihar a kan barkewar cutar COVID-19 a kasar nan.

Kamar yadda yace, kudin ayyukan yau da kullum za a zabtare kashi 40 daga ciki a maimakon albashi da fansho; kuma alawus din masu mukaman siyasa za a zabtare shi da kashi 50.

Coronavirus: Gwamnan APC ya zabtare rabin alawus din 'yan siyasar jiharsa

Coronavirus: Gwamnan APC ya zabtare rabin alawus din 'yan siyasar jiharsa
Source: UGC

DUBA WANNAN: Gwamnan APC ya nada yaro mai shekaru 15 a matsayin sarki mai daraja ta daya a jiharsa

Ya nuna damuwarsa ta yadda wasu suka ki dakatar da shagulgula da kuma al’adu tare da kasa rufe wasu makarantun kamar yadda ya bada umarni. Hakan kuwa ya ce so ake a ga matakin da gwamnati za ta dauka tare da saka rayukan jama’ar jihar cikin hatsari.

“Na umarci jami’an tsaro da su fara daukar mataki a kan duk wanda suka kama yana take doka. Idan kuma al’amura suka ci gaba da tafiya a hakan, bamu da zabin da ya wuce mu rufe duk wasu al’amura na jihar don tseratar da rayukan jama’a.

“Don tabbatar da jama’a sun bi dokar, zan kafa kwamiti wanda ni zan jagoranta don dubawa tare da tantance cutar a jihar nan,” yace.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Nigeria

Online view pixel