Coronavirus: Gwamnatin Kano ta hana manyan motocin daukar fasinjoji shiga jahar

Coronavirus: Gwamnatin Kano ta hana manyan motocin daukar fasinjoji shiga jahar

- Gwamnatin Kano ta bayar da umarnin dakatar da manyan motoci da ke daukar fasinjoji masu zuwa Kano daga Legas shiga jahar

- Hakan na daga cikin yunkurin hana yaduwar cutar coronavirus a jahar

- Gwamnatin ta ce ta haramta wa motocin shiga jahar sakamakon motocin na daukar mutane masu dimbim yawa wanda hakan zai iya sa wa a samu bullar cutar

Gwamnatin jahar Kano karkashin jagorancin Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ta bayar da umarnin dakatar da manyan motoci da ke daukar fasinjoji masu zuwa Kano daga jahar Legas shiga jahar.

Hakan na daga cikin yunkurin hana yaduwar cutar coronavirus da gwamnatin Kano ke yi.

Coronavirus: Gwamnatin Kano ta hana manyan motocin daukar fasinjoji shiga jahar
Coronavirus: Gwamnatin Kano ta hana manyan motocin daukar fasinjoji shiga jahar
Asali: UGC

Gwamnatin ta bayyana cewa ta haramta wa motocin kirar Luxurious shiga jahar sakamakon motocin na daukar mutane masu dimbim yawa wanda hakan zai iya sa wa a samu bullar cutar.

KU KARANTA KUMA: Jerin manyan mutanen da suka yi cudanya da Abba Kyari kafin a tabbatar ya kamu da Coronavirus

A bangare guda mun ji cewa Majalisar Malamai da Limaman jihar Kaduna sun bukaci dakatad da Sallar Juma'a da Khamsu-Salawati idan mamu sun zarce mutane 20 a fadin jihar saboda annobar COVID-19. Sakatare Janar na majalisar, Malam Yusuf Arrigasiyyu, a jawabin da ya sake ranar Talata a Kaduna, ya shawarci dukkan Masallatan Juma'a su dakatar.

A cewarsa “Muna bada shawaran cewa dukkan Masallatan Juma'a da Khamsu-Salawati da adadin mamu ya zarce 20 su dakatar har sai lokacin da aka sanar a bude.“

“Majalisar ta jaddada cewa sun dau wannan mataki ne bisa ga koyarwan Manzon Allah (SAW).“

“Hakazalika muna kira ga mutan jihar Kaduna su bi umurnin likitoci a koda yaushe kuma su guji yada cutar coronavirus.“

Arrigasiyu ya jinjinawa gwamnatin jihar Kaduna kan matakan da ta dauka wajen hana shigowar cutar jihar Kaduna.

Majalisar ta yi kira ga mutane su taimakawa makwabtansu da wannan kulle zai shafa musamman bangaren kayan abinci da rayuwar yau da kullum.

Ya bukaci yan uwa Musulmai su kasance cikin addua da kai dauki wajen Allah don kawar mana da wannan cutar.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel