Gwamnan APC ya nada yaro mai shekaru 15 a matsayin sarki mai daraja ta daya a jiharsa

Gwamnan APC ya nada yaro mai shekaru 15 a matsayin sarki mai daraja ta daya a jiharsa

- Majalisar zartarwa ta jihar Ondo ta amince da nadin yarima Oloyede Adeyeoba, mai shekaru 15, a matsayin Arujale na Okelsi Okeluse a karamar hukumar Ose

- Nadin na daya daga cikin nadin sarakuna uku da gwamnan jihar Ondo, Oluwarotimi Akeredolu, ya amince da su a ranar Litinin

- Fagbemi ya ce majalisar zartarwa ta yi nazari mai zurfi kafin amincewa da nadin matashin a matsayin magajin mahaifinsa

Majalisar zartarwa ta jihar Ondo ta amince da nadin yarima Oloyede Adeyeoba, mai shekaru 15, a matsayin Arujale na Okelsi Okeluse a karamar hukumar Ose.

Matashin ya kasance da daya tilo ga tsohon sarkin da ya mutu, kamar yadda rahotanni suka bayyana.

Nadin na daya daga cikin nadin sarakuna uku da gwamnan jihar Ondo, Oluwarotimi Akeredolu, ya amince da su a ranar Litinin.

Sauran nadin da gwamnan ya amince da su sun hada da nadin yarima Ebenezer Adewunmi a matsayin Olupenmen na Upenmen a yankin karamar hukumar Owo na jihar.

Gwamnan APC ya nada yaro mai shekaru 15 a matsayin sarki mai daraja ta daya a jiharsa

Gwamnan APC ya nada yaro mai shekaru 15 a matsayin sarki mai daraja ta daya a jiharsa
Source: Twitter

DUBA WANNAN: Boko Haram: Yadda muka yi asarar zaratan sojoji 47 a harin kwanton bauna - Rundunar soji

Da yake gabatar da jawabi ga manema labarai bayan kammala taron majalisar zartarwa, kwamishinan kananan hukumomi, Lola Fagbemi, tare da kwamishinan yada labarai, Donald Ojogo, sun ce nadin matashin ya biyo bayan kada kuri'ar amincewa a tsakanin manyan masu hannu a nada sarkin masarautar.

Fagbemi ya ce majalisar zartarwa ta yi nazari mai zurfi kafin amincewa da nadin matashin a matsayin magajin mahaifinsa.

A wani labari na daban, a ranar Talata ne hedikwatar rundunar tsaro ta kasa (DHQ) ta bayyana cewa ta yi asarar zaratan dakarun soji 47, sabanin 70 da wasu rahotanni suka bayyana cewa an kashe ranar Litinin, yayin wani harin da mayakan Boko Haram suka kai wa rundunar sojoji.

Kazalika, DHQ ta bayyana cewa dakarun soji 15 ne suka samu raunuka yayin harin kwanton baunar da 'yan kungiyar ta Boko Haram suka kai wa sojoji a Gorgi da ke dajin Allargano a jihar Borno.

Da yake karin bayani a kan adadin dakarun sojin da suka mutu da wadanda suka samu rauni, mai kula da bangaren watsa labarai a rundunar soji da ke yaki da ta'addanci a jihar Borno, Manjo Janar Enenche, ya ce ba yayin musayar wuta da 'yan ta'adda aka kashe sojojin ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel