Rudani da firgici a Kano: An hana fasinjoji fita daga jirgi saboda samun marar lafiya

Rudani da firgici a Kano: An hana fasinjoji fita daga jirgi saboda samun marar lafiya

Fasinjojin da ke jirgin kamfanin Air Peace wanda ya taso daga Legas a ranar Talata an hana su fita daga jirgin a filin sauka da tashin jiragen sama na Malam Aminu Kano.

Hakan ya biyo bayan ganowa da aka yi cewa wani fasinja bashi da lafiya a yayin da ake kan hanyar isowa Kano daga Legas din.

Majiyoyin jaridar Daily Trust sun tabbatar da cewa matukin jirgin da ya gano akwai mara lafiya a cikin fasinjojin, ya sanar da hukumomin filin saukar jirgin kafin isowarsu.

Bayan kuwa isowarsu, shugaban jirgin ya hana jama'a sauka har sai da aka tabbatar da cewa fasinjan baya dauke da muguwar cutar coronavirus.

Tuni kuwa hankula suka matukar tashi don hatta ma'aikatan sun bar inda jirgin yake don tsoron haduwa da fasinjan mara lafiya wanda ake zargin ko cutar ce ke damunsa.

Wata majiya mai karfi daga filin jirgin ta sanar da cewa an dau mintoci a hakan kafin ma'aikatan lafiya da ke jirgin su iso tare da yin awon gaba da mara lafiyan zuwa wajen gwajin cutar COVID-19 a filin jirgin.

Rudani da firgici a Kano: An hana fasinjoji fita daga jirgi saboda samun marar lafiya

Rudani da firgici a Kano: An hana fasinjoji fita daga jirgi saboda samun marar lafiya
Source: UGC

DUBA WANNAN: Boko Haram: Yadda muka yi asarar zaratan sojoji 47 a harin kwanton bauna - Rundunar soji

Majiyar ta ce fasinjan mai shekaru 17 ya bayyana da tsoron jirgi ne saboda wannan ne karo na farko da ya fara hawa jirgin sama. Ya kara da cewa matashin da ya bayyana baya dauke da cutar, ya fara amai ne bayan jirgin na sauka kasa.

Daraktan kare abinci na NCAA, Malam Adamu Abdullahi, wanda ya tabbatar da aukuwar lamarin ga manema labarai, ya ce babu wani fasinja mai dauke da cutar a jirgin amma dai wani matshi ya bayyana da rashin lafiya.

Ya ce, dalilin da yasa matukin jirgin ya rufe jirgin shine don ya tabbatar da cewa fasinjojin sun tafi hankalinsu kwance.

Malam Adamu ya ce, "Gaskiyar zance shine an samu 'yar matsala a cikin jirgin. Wani matashi ne da ya fara hawa jirgi a yau ya dinga amai bayan jirgin ya sauka. Shugabannin jirgin sun hana fita ne don kowa ya tabbatar da cewa ba cutar ce yake fama da ita ba."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel