Yanzu-yanzu: Osinbajo ya killace kansa bayan ya zauna kusa da Kyari a FEC

Yanzu-yanzu: Osinbajo ya killace kansa bayan ya zauna kusa da Kyari a FEC

- Mataimakin shugaban kasar Najeriya Farfesa Yemi Osinbajo ya killace kansa

- Osinbajo da Kyari sun zauna kusa da juna ne a taron majalisar zartarwa ta tarayya da aka yi na karshe a fadar shugaban kasa

- Kyari, wanda shine shugaban ma’aikatan fadar shugaba Buhari na dauke da cutar COVID-19

Wani rahoto da jaridar Daily Sun ta ruwaito ya bayyana cewa, mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo ya killace kansa.

Kamar yadda rahoton ya bayyana, shugaban ma’aikatan mataimakin shugaban kasar, Ade Ipaye, wanda shima babban lauya ne, ya killace kansa.

Osinbajo da Kyari dai suna zauna gab da juna ne a taron majalisar zartarwar da aka yi na karshe a fadar shugaban kasar.

Yanzu-yanzu: Osinbajo ya killace kansa bayan ya zauna kusa da Kyari a FEC

Yanzu-yanzu: Osinbajo ya killace kansa bayan ya zauna kusa da Kyari a FEC
Source: Twitter

DUBA WANNAN: Abba Kyari: Shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasa ya kamu da Coronavirus

Kyari, wanda shine shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasar ya bayyana dauke da mugunyar cutar coronavirus din.

Kyari wanda yayi tafiya zuwa kasar Jamus a ranar Asabar 7 ga watan Maris, ya hadu da jami'an Siemens ne a Munich a kan wani shiri na fadada wutar lantarkin Najeriya. Ya dawo kasar nan a ranar Asabar, 14 ga watan Maris.

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Abubakar Atiku, ya tura gajeren sako ga Kyari a yau Talata inda yaka masa fatan alheri. "Tunanina da addu'o'ina suna tare da shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasa, Abba Kyari. Allah ya kare mu gabaki daya, kuma ya bashi lafiya," ya wallafa a shafinsa na twitter.

Wasu 'yan Najeriya kuwa sun yi martani suna cewa wannan annobar za ta koya wa shugabannin Najeriya darasi ne. Su san cewa cibiyoyin kiwon lafiya na zamani ne mafita ga kowacce al'umma.

Jama'a da yawa suna ta ba'a ga shugabannin tare da jaddada cewa ba damar fita kasar waje yawon shakawata ballantana kuma zuwa asbiti a wannan lokaci.

A halin yanzu, an dage zaman majalisar zartarwar kasar nan har sai baba ta gani.

Hakazalika, a matsayin hanyar kariya daga yaduwar muguwar cutar coronavirus, gwamnatin tarayya ta umarci dukkan ma'aikatanta da su yi aikinsu daga gida daga yau Talata, 24 ga watan Maris din 2020.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel