Kwamishinan lafiya ya bayyana sunan Dino Melaye a cikin wadanda ake zargin sun kamu da coronavirus

Kwamishinan lafiya ya bayyana sunan Dino Melaye a cikin wadanda ake zargin sun kamu da coronavirus

- Gwamnatin jihar Legas ta bukaci duk wadanda suka halarci bikin shagalin African Magic Viewers’ Choice Award da su killace kansu

- Wannan na kunshe ne a wallafar da kwamishinan lafiya na jihar Legas, Farfesa Akin Abayomi yayi a twitter a ranar Talata

- Wadanda suka samu halartar wajen sun hada da Sanata Dino Melaye, Bisola Aiyeola, Basketmouth, Ebuka Obi-Uchende, Toke Makinwa, Denola Grey, Banky Wellington da matarsa Adesua.

Gwamnatin jihar Legas ta bukaci duk wadanda suka halarci bikin shagalin African Magic Viewers’ Choice Award karo na 7 wanda aka yi a ranar 14 ga watan Maris 2020, su killace kansu don zai yuwu sun samu haduwa da mai cutar COVID-19.

Wannan na kunshe ne a wallafar da kwamishinan lafiya na jihar Legas, Farfesa Akin Abayomi yayi a twitter a ranar Talata, kamar yadda jaridar Daily Trust ta bayyana.

Kamar yadda jawabin ya bayyana, “Ina sanar da duk wadanda suka halarci bikin African Magic Viewers Choice Award wanda aka yi a ranar 14 ga watan Maris a Eko Hotels, a kan cewa zai yuwu sun ci karo da mai cutar coronavirus kuma akwai yuwuwar sun dauka cutar.”

Jaridar Daily Trust ta bayyana cewa, manyan mutane sun halarci wajen taron wadanda suka kunshi manyan ‘yan wasan kwaikwayo da manyan ‘yan jaridu.

A bikin an samu nishadantarwa daga manyan mawakan Afrika da suka hada da 2Baba Idibia, Osang Abang da kuma Cobhams, wanda yayi wakar ta’aziyyar manyan jaruman Nollywood da suka riga mu gidan gaskiya.

Kwamishinan lafiya ya bayyana sunan Dino Melaye a cikin wadanda ake zargin sun kamu da coronavirus
Kwamishinan lafiya ya bayyana sunan Dino Melaye a cikin wadanda ake zargin sun kamu da coronavirus
Asali: UGC

DUBA WANNAN: Abba Kyari: Shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasa ya kamu da Coronavirus

Hakazalika, taurari kamar su Toyin Abraham, Timin Egbuson, Dakore Egbuson-Akande, Funke Akindele da sauransu sun halarta.

Mercy Eke da Mike Edwards na shirin Big Brother Africa sun samu halarta har sun karba lambar yabo.

Sauran sanannun da suka samu halartar wajen sun hada da Sanata Dino Melaye, Bisola Aiyeola, Basketmouth, Ebuka Obi-Uchende, Toke Makinwa, Denola Grey, Banky Wellington da matarsa Adesua.

Kwamishinan lafiyan jihar legas din ya shawarcesu da su killace kansu sannan sunkira lambobin gaggawa idan sun bayyana da wata alama ta cutar COVID-19. Ya kara da kira a garesu da su daina shiga mutane don gujewa yaduwar muguwar cutar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel