Bayan fitowar sakamakon gwajin da aka yi masa na yiwuwar kamuwa da cutar Coronavirus, shugaba Muhammadu Buhari ya shiga ganawa da hafsoshin tsaro a fadar shugaban kasa, Aso Villa, Abuja.
Ana cikin ganawar lokacin kawo wannan rahoton.
Wadanda ke hallare a ganawar sune mai bada shawaran kan lamarin tsaro, Babagana Munguno (mai murabus), Dirakta janar na DSS, Yusuf Bichi da Sifeto janar na hukumar yan sanda, Mohammed Adamu.

Yanzu-yanzu: Bayan fitowar sakamakon gwajinsa, Buhari ya shiga ganawa da hafsoshin tsaro
Source: Facebook
Mun kawo muku rahoton cewa Sakamakon gwajin da aka yi wa Shugaba Muhammadu Buhari na Covid-19 ya nuna cewa shugaban baya dauke da kwayar cutar kamar yadda Thisday ta ruwaito.
Hukumar NCDC ta sanar da shugaban kasar cewa ba ya dauke da kwayar cutar a safiyar yau a Abuja.
A cewar wata majiya daga fadar shugaban kasa, gwajin da aka yi ya nuna cewa shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasa, Abba Kyari ya kamu da cutar kamar yadda sakamakon ya nuna a ranar Litinin.
Kyari ya tafi Jamus a ranar Asabar 7 ga watan Maris inda ya gana da wasu jami'an kamfanin Siemens a binrin Munich a kan shirin fadada aikin wutan lantarki a Najeriya.

Kyari
Source: Depositphotos
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng