Coronavirus: Sabon salon aiki da ministan sadarwa, Sheikh Pantami, ya bullo da shi a ofishinsa (Hotuna)
Yin amfani da fasahar zamani ta amfani da kiran waya mai nuna hoto mai motsi, wato 'bidiyo', domin gudanar da taro na daga cikin muhimman hanyoyin gudanar da aiki a yayin da ake fama da annobar cutar coronavirus.
Tun bayan barkewar annobar cutar coronavirus a fadin duniya, gwamnatoci da hukumomi ke bawa jama'a shawarar su killace kansu tare da kauracewa wuraren taron jama'a domin kare kansu daga hatsarin kamuwa da muguwar kwayar cutar coronvirus mai sarke numfashi.
Kasancewar ana iya kamuwa da kwayar cutar corona ta hanyar mu'amala da mai dauke da kwayar cutar ko kuma dabdala a wurin da aka taba samun kwayar cutar, akwai bukatar ma'aikatan gwamnati su rage yawan ganawa gemu da gemu a tsakaninsu domin dakile yaduwar kwayar cutar coronavirus.
DUBA WANNAN: Gwajin coronavirus: Abinda Masari ya yi bayan ganawa da Buhari a Villa
Bisa la'akari da haka ne yasa ministan sadarwa da tattalin arziki na fasahar zamani, Dakta Isa Ali Pantami, ya bullo da hanyar gudanar da aiki da ganawar ma'aikatan gwamnatin tarayya ta hanyar amfani da sadarwa mai amfani da sautin murya da hoto mai motsi.
Ma'aikatar sadarwa tare da hadin gwuiwar daya daga cikin hukumomin da ke karkashinta mai suna 'Galaxy Backbone' ta samar da wannan sabuwar fasaha a ma'aikatu da hukumomin gwamnati da ke Abuja.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng