Na samu sauki daga cutar COVID-19 yanzu Inji Koci Mikel Arteta

Na samu sauki daga cutar COVID-19 yanzu Inji Koci Mikel Arteta

Mun samu labari cewa Kocin Arsenal, Mikel Arteta, ya ce ya samu lafiya sarai daga cutar coronavirus da ya kamu da ita.

Mikel Arteta mai shekaru 37 a Duniya, shi ne Koci na farko da wannan cuta ta fara kamawa a Gasar Firimiya na kasar Ingila.

Kusan makonni biyu da su ka wuce ne aka yi wa tsohon ‘Dan wasan gwaji, inda aka tabbatar da cewa ya kamu da wannan cuta.

Arteta ya bayyanawa na kusa da shi cewa bai jin dadi bayan ya samu labari cewa shugaban kungiyar Olympiakos ya kamu.

Cutar COVID-19 ta kama Evangelos Marinakis ne a farkon Watan Maris – A daidai wannan lokaci Arsenal ta buga wasa da kungiyarsa.

KU KARANTA: Kocin Arsenal Mikel Arteta ya kamu da cutar COVID-19

Na samu sauki daga cutar COVID-19 yanzu Inji Koci Mikel Arteta

Kocin Arsenal Mikel Arteta ya ce ya samu lafiya da COVID-19
Source: Instagram

Arteta ya bayyanawa ‘Yan jarida cewa: “Ta dauke ni kusan kwanaki uku ko hudu kafin in fara samun sauki, ina jin karfi a jikina.”

A halin yanzu, Kocin na Arsenal ya tabbatarwa Manema labarai cewa cutar ta sake shi, kuma ya dawo garau bayan ‘yan kwanaki.

Mai horas da ‘Yan wasan na kungiyar Arsenal ya bayyana wannan ne a lokacin da aka hira da shi a gidan talabijin nan na La Sexta.

An rahoto Arteta ya na cewa: “Yanzu na warke sarai. Tsohon Kocin na Manchester City ya ce: “Ina jin cewa na samu lafiya a jikina.”

Haka zalika su ma ‘Yan wasan Arsenal za su dawo aiki bayan sun shafe kwanaki 14 a killace bayan sun hadu da Kocin na su.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit.ng

Online view pixel