Aisha Buhari ta hana ganin shugaban kasa bayan an gano Abba Kyari na dauke da COVID-19

Aisha Buhari ta hana ganin shugaban kasa bayan an gano Abba Kyari na dauke da COVID-19

Uwargidan shugaban kasa Muhammadu Buhari, Aisha Buhari ta hana ganin shugaban kasa bayan an gano cewa shugaban ma'aikatan fadarsa, Abba Kyari na dauke da mugunyar cutar Coronavirus.

Idan zamu tuna, wasu sassan na kafofin yada labarai sun ruwaito cewa Kyari na dauke da cutar COVID-19.

Amma kuma, a ranar Litinin an gano cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari baya dauke da cutar kamar yadda NCDC ta bayyana.

Kamar yadda rahoton da jaridar Thisday ta ruwaito ya bayyana, akwai yuwuwar Kyari ya kamu da cutar ne bayan da ya kai ziyara kasar Jamus a ranar Asabar, 7 ga watan Maris don taro da jami'an kamfanin Siemens a Munich.

DUBA WANNAN: COVID 19: Ministan lafiya ya yi barazanar bayyana sunayen manyan da suka ki yarda a gwada su

A don haka ne uwargidan shugaban kasar ta saka masa dokar zaman gida.

"Matar shugaban kasar ba ta barin kowa ganinsa. Hatta ofishinsa ta hana shi shiga," wata majiya daga fadar shugaban kasar ta sanar da jaridar Daily Nigerain.

Idan zamu tuna, sakamakon gwajin da aka yi wa Shugaba Muhammadu Buhari na Covid-19 ya nuna cewa shugaban baya dauke da kwayar cutar kamar yadda Thisday ta ruwaito.

Hukumar NCDC ta sanar da shugaban kasar cewa ba ya dauke da kwayar cutar a safiyar yau a Abuja. A cewar wata majiya daga fadar shugaban kasa, gwajin da aka yi ya nuna cewa shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasa, Abba Kyari ya kamu da cutar kamar yadda sakamakon ya nuna a ranar Litinin.

Kyari ya tafi Jamus a ranar Asabar 7 ga watan Maris inda ya gana da wasu jami'an kamfanin Siemens a binrin Munich a kan shirin fadada aikin wutan lantarki a Najeriya.

Rahotanni sun bayyana cewa ya hallarci taron da aka gudanar a kan annibar Covid-19 a Najeriya a ranar Lahadi inda a nan ne ya fara tari.

Daga bisani ya mika kansa domin a yi masa gwaji kuma a jiya Litinin aka sanar da shi sakamakon gwajin. Tuni dai Kyari ya killace kansa tun bayan da ya samu sakamakon gwajin.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel