IMF ta ce COVID-19 za ta ruguza tattalin arzikin kasashe a shekerar bana

IMF ta ce COVID-19 za ta ruguza tattalin arzikin kasashe a shekerar bana

Hukumar IMF mai bada lamuni ta Duniya ta gargadi kasashe cewa za a yi fama da durkushewar tattalin arziki a wannan shekara ta 2020 da ake ciki.

IMF ta bayyana cewa akwai yiwuwar tattalin kasashe su karye a shekarar nan. Hukumar ta tsoratar da cewa rugujewar tattalin arzikin zai yi matukar muni.

A cewar hukumar Duniyar, tattalin arzikin kasashe za su kama hanyar dawowa daidai a shekarar badi ta 2021 bayan kasashe sun durkushe a shekarar nan.

Shugabar hukumar IMF, Kristalina Georgieva ce ta yi wa jawabi a lokacin da ta zanta da Ministocin kudi na manyan kasashen G-20 na Duniya.

Kristalina Georgieva ta kuma tattauna da gwamnonin manyan bankin wadannan kasashe masu karfi a zantawar da ta yi ta wayar salula a makon nan.

KU KARANTA: Gwamnonin Najeriya sun fasa zama bayan karyewar farashin mai

IMF ta ce COVID-19 za ta ruguza tattalin arzikin kasashe a shekerar bana

Tattalin arzikin kasashe zai gamu da cikas saboda Coronavirus
Source: UGC

An yi wannan waya ne a Ranar Litinin kamar yadda Daily Trust ta rahoto. Kristalina Georgieva ta ce: “Tasirin matsin tattalin arziki zai bayyana matuka.”

Georgieva Mai shekaru 66 a Duniya ta fadawa shugabannin wadannan kasashe cewa: “Abubuwa za su murmure da zarar kwayar wannan cutar ta bace”

Haka zalika Misis Georgieva ta shaidawa kasashen na G-20 cewa tattalin arzikin kasashen da su ka bunkasa za su fi samun damar shawo kan matsalar.

A jawabin na ta, Kristalina Georgieva ta nuna cewa kasashen da ke tasowa za su gamu da cikas. Kawo yanzu har annobar ta fara taba kasashe marasa karfi.

Dukiya ta na ficewa daga kasashen da tattalin arzikinsu bai bunkasa ba, don haka IMF ta yi kira ga manyan bankuna su kirkira dabarun da za su taimaka.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit.ng

Online view pixel