Yan bindiga sun kai ma jami’in dake yaki da Coronavirus hari a Nassarawa

Yan bindiga sun kai ma jami’in dake yaki da Coronavirus hari a Nassarawa

Wasu gungun yan bindiga sun kai farmaki a gidan shugaban kwamitin ko-ta-kwana dake yaki da yaduwar annobar nan mai toshe numfashi watau cutar Coronavirus na jahar Nassarawa, Dakta Ibrahim Adamu.

Daily Nigerian ta ruwaito yan fashin sun bi sawun Ibrahim, wanda shi ne daraktan kiwon lafiya a ma’aikatar kiwon lafiya ta jahar Nassarawa, yayin da yake kan hanyarsa ta komawa gida da misalin karfe 1:30 na dare.

KU KARANTA: Majalisar koli ta Musulunci ta bada umarnin kulle Masallatan Abuja saboda Coronavirus

Bayan sun kutsa kai cikin gidan nasa, yan fashin sun kwashe muhimman abubuwa da suka hada da kwamfutar Laptop, makullon motoci, katukan cire kudi da sauran kayayyaki mallakin matarsa.

Da yake tabbatar da harin, jami’in watsa labaru na ma’aikatar kiwon lafiya ta jahar Nassarawa, Abdullahi Ogoshi ya bayyana cewa: “Yan bindiga su 6 sun kutsa kai cikin gidan daraktan da tsakar daren Litinin, inda suka dauke katukan ciren kudinsa na banki da kwamfuta.

“Har ma sai da suka yi barazanar kashe shi idan har suka ga lambobin cirar kudin da ya basu basa aiki. Kwamfutocin da suka kwashe kuwa sun kunshi duk bayanai da matakan da gwamnati za ta dauka a kan cutar Coronavirus.” Inji shi.

A wani labarin kuma, rundunar Yansandan jahar Zamfara ta sanar dakama wani kasurgumin dan bindiga mai suna Sani Boka dake kauyen Masama cikin karamar hukumar Gummi na jahar Zamfara bayan ya kashe surukinsa, sa’anann ya sace ya yi garkuwa da kanwarsa.

Kwamishinan Yansandan jahar, Usman Nagogo ne ya bayyana haka yayin da yake holen mutumin, a babban ofishin Yansandan jahar, wanda da kansa ya bayyana ma yan jaridu laifin da ya aikata.

A cewar Nagogoe, kanwarce ta gane fuskar Sani Boka a lokacin da suka kai musu farmaki, kuma ta shaida ma Yansanda cewa yana daya daga cikin wadanda suka yi garkuwa da ita tare da abokiyar zamanta.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel