Dan bindiga ya kashe surukinsa, ya yi garkuwa da kanwarsa uwa daya uba daya a Zamfara

Dan bindiga ya kashe surukinsa, ya yi garkuwa da kanwarsa uwa daya uba daya a Zamfara

Rundunar Yansandan jahar Zamfara ta sanar dakama wani kasurgumin dan bindiga mai suna Sani Boka dake kauyen Masama cikin karamar hukumar Gummi na jahar Zamfara bayan ya kashe surukinsa, sa’anann ya sace ya yi garkuwa da kanwarsa.

Daily Trust ta ruwaito kwamishinan Yansandan jahar, Usman Nagogo ne ya bayyana haka yayin da yake holen mutumin, a babban ofishin Yansandan jahar, wanda da kansa ya bayyana ma yan jaridu laifin da ya aikata.

KU KARANTA: Annobar Corona: Bankin Access ta garkame ofishinta a Legas bayan bullar cutar

A cewar Nagogoe, kanwarce ta gane fuskar Sani Boka a lokacin da suka kai musu farmaki, kuma ta shaida ma Yansanda cewa yana daya daga cikin wadanda suka yi garkuwa da ita tare da abokiyar zamanta.

“Wannan bayani ne ya bamu daman kama shi, tare da dukkanin yan gungunsu da suka shahara wajen satar mutane tare da fashi da makami. Miyagun sun afka gidsan Alhaji Umar Ibrahim ne dake kauyen Dan-Awo a ranar 1 ga watan Maris.

“Inda suka kashe Alhaji Umar, suka yi awon gaba da matansa biyu, wanda daga cikinsu akwai kanwar Sani Boka, har sai da suka biya kudin fansa naira miliyan 1.8 sa’annan suka sake su. Daga cikin kudin an baiwa Sani Boka N200,000.” Inji shi kwamishinan.

Sauran miyagun da aka kama suna hada da Alhaji Kabiru Lawali, Kabiru Sani, Sani Umar, Abubakar Yakubu da Aminu Abubakar. Kwamishinan ya yi kira ga jama’a dasu ankara saboda a yanzu miyagun suna zaune ne a cikinsu.

Haka zalika kwamishinan yace a ranar 3 ga watan Maris ne suka kama wasu mutane uku Usman Bala, Umar Abubakar da Kabiru Abdullahi dake baiwa yan bindiga bayanan sirri, yace sun kama su ne bayan sun aika ma jama’an kauyen Nassarawa wasika dake cewa su basu N100m ko kuma su kona garin gaba daya.

Kwamishinan yace sun kama miyagun ne ta hanyar bin lambar wayar da suka yi amfani da ita wajen kiran dakacin kauyen Nassarawa, Alhaji Aminu Bello, wanda shi kuma ya shaida ma Yansanda halin da ake ciki.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel