Wata sabuwa: Za mu yi amfani da jami'an tsaro wajen hana taron jama'a - FG

Wata sabuwa: Za mu yi amfani da jami'an tsaro wajen hana taron jama'a - FG

Gwamnatin tarayyar Najeriya ta ce za ta yi amfani da sojoji da 'yan sanda wajen tabbatar da cewa jama'a sun nesanta da junansu domin takaita yaduwar kwayar cutar coronavirus.

Ministan yada labarai da al'adu na kasa, Lai Mohammed, ne ya sanar da hakan yayin wata ganawarsa da manema labarai a Abuja ranar Litinin.

Ministan ya ga baiken wasu jagorori da malaman addinai da suka yanke shawarar yin watsi da umarnin gwamnatin tarayya na hana taron jama'a masu yawa.

Wasu masallatai da coci-coci sun gudanar da taron ibada na ranar Juma'a da Lahadi kamar yadda suka saba duk da umarnin da gwamnati ta bayar na a rufe wuraren ibada a matsayin matakin dakile yaduwar kwayar cutar corona.

A cewar ministan, "gwamnatin tarayya tana sane da cewa wasu shugabannin addini da siyasa sun ki yin biyayya ga umarnin gwamnati na hana taron jama'a da yawa.

Wata sabuwa: Za mu yi amfani da jami'an tsaro wajen hana taron jama'a - FG
Lai Mohammed
Asali: Facebook

"Akwai bukatar dukkan shugabanni su hada kai a lokaci irin wannan. Dole su guji jefa rayuwar mabiyansu da sauran jama'a a cikin hatsari.

"Akwai bukatar dukkan 'yan Najeriiya su kiyaye, su kuma kula da kansu, tare da daina zargin wasu da yi musu wata makarkashiya. Ga wadanda suke ganin za su cigaba da karya dokokin da gwamnati kirkira domin dakile wannan annoba, nan bada dadewa ba dogon hannun hukuma zai kama su."

DUBA WANNAN: COVID-19: Yadda Bill Gates yayi hasashen annobar a 2015 da 2018 (Bidiyo)

Ministan ya bayyana cewa kwamitin da shugaba kasa, Muhammadu Buhari, ya kafa a kan bullar annobar coronavirus zai fito da jerin wasu sabbin dokoki, kuma da zarar sun fito za a sanar da jama'a.

Kazalika, ya kara da cewa dukkan dokokin da za a kirkiresu ne domin kare 'yan Najeriya daga hatsarin annobar kwayar cutar corona da ke cigaba da mamaya a cikin kasa da duniya baki daya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel