Yan bindiga sun kaddamar da hari a Neja, sun kashe jami’in Dansanda, sun harbi Sojoji

Yan bindiga sun kaddamar da hari a Neja, sun kashe jami’in Dansanda, sun harbi Sojoji

Wasu gungun miyagun yan bindiga sun kai farmaki a kauyukan Galkogo da Zumba dake cikin karamar hukumar Shiroro na jahar Neja, inda suka kashe wani jami’in Dansanda, tare da harbin Yansanda 3.

Gidan talabijin na Channels ta ruwaito jami’in hulda da jama’a na rundunar Yansandan jahar, ASP Waslu Abiodun ne ya bayyana haka a ranar Lahadi, inda yace yan bindigan sun kai farmakin ne a kan babura fiye da 50 kuma sun kwashe fiye da sa’o’i biyu sun cin karensu babu babbaka.

KU KARANTA: Muna aiki a kan allurai 20 da zasu magance annobar Coronavirus – Cibiyar WHO

Yan bindiga sun kaddamar da hari a Neja, sun kashe jami’in Dansanda, sun harbi Sojoji
Yan bindiga sun kaddamar da hari a Neja
Asali: Facebook

Mazauna kauyukan sun bayyana cewa baya ga jami’an tsaron da yan bindigan suka kai ma hari, sun harbi wata karamar yarinya a ciki, sai kuma wani mutumi da suka harba a cinya, sa’annan sun yi awon gaba da jama’a da dama.

Sanata mai wakiltar yankin a majalisar dattawan Najeriya, Sanata Sani Musa ya aika ma majiyar Legit.ng wasu bidiyon harin da yan bindigan suka kai, inda ya bayyana damuwarsa game da halin rashin tsaro da al’ummarsa suke ciki.

Sanata Sani Musa ya bayyana cewa al’ummar kananan hukumomin Shiroro, Munya, Rafi da Paikoro ne suka fi fuskantar wannan matsalar ta tsaro a sanadiyyar yan bindiga da masu garkuwa da mutane da suka mamaye yankunan.

Sanatan ya kara da cewa da dama daga cikin jama’an sun tsere daga gidajensu sun nemi mafaka a cikin dazuka, amma yace an mika wadanda suka jikkata a sanadiyyar harin zuwa asibitin kwararru na IBB dake garin Minna domin samun kulawa.

Daga karshe mai magana da yawun rundunar Yansandan jahar ya ce tuni kwamishinan Yansandan jahar, Adamu Usman ya tura da jami’an Yansanda zuwa yankin domin tabbatar da tsaro.

A wani labarin kuma, dan tsohon mataimakin shugaban kasa, kuma tsohon dan takarar shugabancin Najeriya a karkashin inuwar jam’iyyar APC da PDP, Alhaji Atiku Abubakar, ya kamu da cutar annobar Coronavirus.

Alhaji Atiku Abubakar da kansa ya bayyana haka a shafinsa na kafar sadarwar zamani na Facebook, a daren Lahadi, 22 ga watan Maris, inda yace tuni suka garzaya da dan nasa zuwa asibiti domin samun kulawa.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng