Sarki Salmanu ya sanya dokar ta baci na tsawn kwanaki 21 saboda Coronavirus

Sarki Salmanu ya sanya dokar ta baci na tsawn kwanaki 21 saboda Coronavirus

Mai alfarma Sarkin Saudiyya, Sarki Salman bin Abdulaziz ya sanya dokar hana shige da fice a kafatanin kasar Saudiyya daga karfe 7 na dare zuwa 6 na safiyar kowanne rana na tsawon kwanaki 21 don rage yaduwar cutar Coronavirus.

Jaridar Alarabiya ce ta ruwaito kamfanin dillancin labaru na kasar Saudiyya ta fitar da sanarwar, wanda tace umarnin Sarkin zai fara aiki ne daga ranar Litinin, 23 ga watan Maris na shekarar 2020.

KU KARANTA: Muna aiki a kan allurai 20 da zasu magance annobar Coronavirus – Cibiyar WHO

Sanarwar ta kara da cewa ma’aikatan kula da al’amuran cikin gida ce za ta tabbatar da dabbaka dokar tare da hadin kan hukumomin Soji, Yansanda da sauran hukumomin farin kaya da aikin tabbatar da bin doka ya shafa.

Gwamnatin ta nemi jama’a su zauna a gidajensu a lokacin dokar, kada wanda ya fito har sai ta kama, kamar domin duba lafiyarsu. Sai dai dokar ta daga kafa ga muhimman ma’aikatan gwamnati da na kamfanoni masu zaman kansu.

Daga cikin wadanda dokar ta daga ma kafa akwai jami’an tsaro, Sojoji, yan jaridu, ma’aikatan kiwon lafiya, jami’an ma’aikatun kudi, jami’an kamfanonin sadarwa da kuma jami’an hukuara ruwan sha ta kasar.

Gwamnatin ta dauki wannan mataki ne sakamakon samun hauhawar masu kamuwa da cutar a Coronavirus a kasar Saudiyya, inda a yanzu adadinsu ya kai mutum 511, kamar yadda kaakkain ma’aikatan kiwon lafiya na kasar, Mohamemd Al-Abd al-Ali ya bayyana.

A wani labarin kuma, dan tsohon mataimakin shugaban kasa, kuma tsohon dan takarar shugabancin Najeriya a karkashin inuwar jam’iyyar APC da PDP, Alhaji Atiku Abubakar, ya kamu da cutar annobar Coronavirus.

Alhaji Atiku Abubakar da kansa ya bayyana haka a shafinsa na kafar sadarwar zamani na Facebook, a daren Lahadi, 22 ga watan Maris, inda yace tuni suka garzaya da dan nasa zuwa asibiti domin samun kulawa.

“Sakamakon gwaji ya tabbatar da Da na yana dauke da kwayar cutar Coronavirus, mun sanar da hukumar kula da yaduwar cututtuka ta Najeriya, kuma mun garzaya da shi zuwa asibitin koyarwa na Gwagwalada domin kulawa da shi.” Inji shi.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng