Bayan an yi mata rigakafin COVID-19, Angela Merkel za ta rufe kanta a gida

Bayan an yi mata rigakafin COVID-19, Angela Merkel za ta rufe kanta a gida

Mun samu labari daga kasar waje cewa shugabar kasar Jamus, Angela Merkel, za ta rufe kanta a gida bayan da wani Likita mai dauke da cutar Coronavirus ya duba ta.

Gidan yada labarai na AFP ya bayyana cewa Angela Merkel za ta killace kanta da kanta ne a sakamakon haduwa da ta yi da wani Likita da ya kamu da COVID-19.

Kwanakin baya ne wani Likita ya ziyarci shugabar kasar ta Jamus, inda ya yi mata rigakafafin wannan cuta mai hana numfashi wanda ta kashe Bayin Allah da-dama.

Bayan an yi wa wannan Malamin asibiti gwaji daga baya, an gano cewa shi kansa ya na dauke da cutar COVID-19, a dalilin haka Merkel ta dauki matakin kare lafiyarta.

Mai magana da yawun bakin gwamnatin Jamus ya bada sanarwar cewa shugabar kasar za ta rufe kanta, sannan za a rika yi mata gwaji domin tabbatar da lafiyarta.

Steffen Seibert ya bayyana cewa shugaba Angela Merkel za ta koma aiki daga gida har zuwa lokacin da Malaman asibiti za susamu sakamakon gwajin da za ayi mata.

KU KARANTA: Coronavirus ta shiga Jihohi 5 a Najeriya amma Shugaba Buhari ya ki magana

A jawabin na sa, Seibert ya nuna cewa za a dauki lokacin kafin a tabbatar da halin lafiyar shugabar kasar. A halin yanzu dai za ta koma aikin na ta ne daga dakinta.

Kakakin gwamnatin ya bayyana cewa a shekaru 15 da Merkel ta yi a ofis, ta nuna cewa ita mutum ce mai cikakken koshin lafiya duk da rade-radin da wasu ke yi kwanaki.

A nan gida Afrika kuma, shugaban kasar Botsawana ya dauki matakin yin nesa da jama’a, inda zai shafe akalla makonni biyu a killace bayan ya dawo daga kasar waje.

A halin yanzu shugaba Eric Masisi zai rika aiki ne daga gida kamar yadda Africa News ta bayyana. An kebe shugaban daga Iyalinsa bayan dawowarsa daga Namibia.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit.ng

Online view pixel