Allah ya yi min wahayi game da cutar coronavirus – Babban Fasto

Allah ya yi min wahayi game da cutar coronavirus – Babban Fasto

Babban shugaban cocin RCCG na kasa wato Fasto Enoch Adeboye ya bayyana cewa Allah ya yi masa wahayi a kan cutar coronavirus.

A cewar Adebayo, ya na daga cikin dalilan da ya sa ya yi umurni ga mabiyan sa da su yi azumin kwana 50 daga watan Janairu.

Fasto ya kuma kara da cewa Allah ya yi masa wahayin cewa zai sa duk duniya a tafi hutun dole a wannan shekara wanda shine ya sa aka ga kasashe suna garkame iyakokin su, sannan ana tilasta wa mutane zaman gida don dole.

Allah ya yi min wahayi game da cutar coronavirus – Babban Fasto

Allah ya yi min wahayi game da cutar coronavirus – Babban Fasto
Source: Twitter

Da ya ke jawabi ga mambobin coci a ranar Lahadi, Adeboye ya ce bai sanar da hakan ba a jawabinsa na sabuwar hekara saboda ya zata zai zo ne a sufar hare-haren ta’addanci.

“Na ji wani manzon Allah ya ce min cutar coronavirus zai mutu, nace masa Amin. Sannan naji kuma wani manzon yana ce mini za a ruwan sama na kwana bakwai da zai wanke cutar a duniya, sai nace Amin. Sai dai kuma ba zai tafi ba kwata-kwata a duniya.

"Wannan cuta ta coronavirus Allah ne da kansa yake nuna wa duniya cewa shine mai iko akan komai. Yan iya yin yadda yasa a kowani lokaci sannan da tuantar da su da su dawo ga Allah.

“Ina so kusa ni cewa babu wanda wannan cuta zai kama idan ya yarda da Allah ne zai kare shi kuma yana karkashin kiyayewan Allah ne. Abinda zaka yi shine ka kiyaye ka kuma koma ga Allah. yin hakan shine zai samar maka da kariya."

Akarshe Adeboye ya ce lallai wannan cutar za ta zo ta wuce nan ba da dadewa ba.

KU KARANTA KUMA: Legas ta sha gaban Jihohin Najeriya a barnar annobar Coronovirus

A wani labarin kuma mun ji cewa a yau Lahadi, gwamnatin tarayya ta sanar da cewa na samu karin mutane uku masu dauke cutar coronavirus (COVID-19), yanzu adadin masu cutar a Najeriya 30.

Hukumar takaita yaduwar cututtuka (NCDC) ta sanar da hakan da safiya Lahadi a shafin raayi da sada zumuntarta na Tuwita.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel