Shugabanni su na magana a kan Coronavirus, Buhari ya yi gum a Najeriya

Shugabanni su na magana a kan Coronavirus, Buhari ya yi gum a Najeriya

Har yanzu ‘Yan Najeriya su na jiran tsammanin lokacin da shugaban kasarsu zai fito ya yi masu bayani game da cutar nan ta Coronavirus da ta barke a Duniya.

Bayan tsawon kusan watanni uku da barkewar wannan cuta, har yanzu shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari bai fito ya yi wa ‘Yan kasarsa jawabi ba.

Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da shugabannin Nahiyar Afrika da sauran kasashen Duniya su su ke fadawa Mabiyansu irin kokarin da su ke yi a halin yanzu.

Premium Times ta fitar da rahoto a Ranar Lahadi, 22 ga Watan Maris ta ce Takwarorin Buhari irinsu Cyril Ramaphosa da Yoweni Museveni duk sun yi jawabai.

Jaridar ta bayyana duk da kokarin da hukumomi da ma’aikatun Najeriya su ke yi na ganin an dakile yaduwar cutar, shugaba Buhari bai ce uffan ba tukuna har yau.

KU KARANTA: COVID - 19: Gwamnan Legas ya fadawa Ma'aikata su yi zamansu a gida

Shugabanni su na magana a kan Coronavirus, Buhari ya yi gum a Najeriya

Shugaba Muhammadu Buhari bai yi wa 'Yan kasa jawabi ba tukuna
Source: Facebook

Duk da ganin wannan annoba ta shiga Jihohi biyar, wannan bai sa shugaba Muhammadu Buhari ya yi magana ba, akasin abin da ake gani a sauran kasashen waje.

A karshen makon nan ne ake sa ran cewa shugaban kasar Uganda, Yoweni Museveni zai sake yi wa ‘Yan kasarsa jawabi. Sau uku kenan ‘Yan kasar na ji daga gare sa.

Haka zalika shugaba Nana Akufo-Addo ya yi wa mutanen kasar Ghana magana sau uku a cikin ‘yan kwanakin nan. Kusan dai haka shugabanni da-dama su ka yi.

Shugabannin Kasar Afrika ta Kudu, Ruwanda, Zimbabwe, Masar da Moroko sun fito sun yi jawabi ga ‘Yan kasarsu sau biyu. Har yanzu tsit ake ji a babar fadar Najeriya.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit

Online view pixel