Ku zauna a gida: Gwamnatin jihar Legas ta bawa dukkan ma'aikatanta hutu saboda coronavirus
Gwamnatin jihar Legas ta bawa dukkan ma'aikatanta; daga kan mataki na daya zuwa na 12, umarnin su zauna a gida na tsawon kwanaki 14 masu zuwa.
Gwamnan jihar Legas, Babajide Sanwo Olu, ne ya sanar da hakan yayin da yake gabatar da karin jawabi a kan bullar annobar kwayar cutar corona a jiharsa ranar Lahadi.
Ya bayyana cewa ma'aikatan zasu cigaba da zama a gida ne na tsawon kwanaki 14 masu zuwa.
A cikin makon da muka yi bankwana da shine gwamnatin jihar Legas ta bayar da umarni rufe dukkan makarantu da wuraren ibada da ke jihar.
Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da adadin masu kamuwa da kwayar cutar corona ke karuwa a jihar.
A yau Lahadi, gwamnatin tarayya ta sanar da cewa na samu karin mutane hudu masu dauke cutar coronavirus (COVID-19), yanzu adadin masu cutar a Najeriya 26.
Hukumar takaita yaduwar cututtuka ta kasa (NCDC) ta sanar da hakan da safiya Lahadi a shafin ra'ayi da sada zumuntarta na Tuwita.
Jawabin yace “Misalin karfe 08:05am na ranar 22 ga Maris, an tabbatar da karuwar masu dauke da cutar Coronavirus, wanda yanzu haka yawansu ya kai 26 a Najerita. Daga cikinsu an sallami biyu da suka samu sauki.“
DUBA WANNAN: An kama wasu ma'aurata da laifin aikata jima'i a cikin mota
A ranar Asabar ne Legit.ng ta wallafa rahoton cewa ministan lafiya, Dakta Osagie Ehanire, ya bayyana cewa an samu karin mutane 10 da suka kamu da cutar Coronavirus a Najeriya.
Ministan ya bayyana hakan ne a shafinsa na Tuwita ranar Asabar, 21 ga watan Maris, 2020.
Yayinda aka samu karuwar mutane bakwai a Legas, sauran ukun na birnin tarayya Abuja.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng