Yanzu-yanzu: An samu karin masu cutar Coronavirus 4 a yau Lahadi

Yanzu-yanzu: An samu karin masu cutar Coronavirus 4 a yau Lahadi

A yau Lahadi, gwamnatin tarayya ta sanar da cewa na samu karin mutane hudu masu dauke cutar coronavirus (COVID-19), yanzu adadin masu cutar a Najeriya 26.

Hukumar takaita yaduwar cututtuka (NCDC) ta sanar da hakan da safiya Lahadi a shafin raayi da sada zumuntarta na Tuwita.

Jawabin yace “Misalin karfe 08:05 am na ranar 22 ga Maris, an tabbatar da asu dauke da cutar Coronavirus 26 a Najerita. Cikinsu an sallami biyu da suka samu sauki.“

“Don sanin adadin wadanda suka kamu da cutar, ku garzaya http://covid19.ncdc.gov.ng“

Yanzu-yanzu: An samu karin masu cutar Coronavirus 4 a yau Lahadi
Yanzu-yanzu: An samu karin masu cutar Coronavirus 4 a yau Lahadi
Asali: Facebook

A jiya mun kawo muku rahoton cewa A bangare guda, Ministan lafiya, Dakta Osagie Ehanire, ya bayyana cewa an samu karin mutane 10 da suka kamu da cutar Coronavirus a Najeriya.

Ministan ya bayyana hakan ne a shafinsa na Tuwita ranar Asabar, 21 ga watan Maris, 2020.

Yayinda bakwai aka samu a Legas, sauran ukun na birnin tarayya Abuja.

Yanzu dai akwai jimillar masu cutar 22 a Najeriya kuma an sallami biyu da suka samu sauki.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng