Cutar Coronavirus ta kama Maldini, Dybala da Fellaini a Italiya da Sin

Cutar Coronavirus ta kama Maldini, Dybala da Fellaini a Italiya da Sin

Rahottani sun zo mana cewa ‘Dan wasan gaban Juventus Paulo Dybala ya kamu da cutar Coronavirus. Wannan ya sa ya zama mutun na uku da ya kamu da cutar a kungiyar.

Idan ba ku manta ba kwanakin baya kun ji cewa Blaise Matuidi ya na dauke da cutar COVID-19. Kafinsa kuma Daniele Rugani ya zama ‘Dan wasan farko da ya kamu da wannan cuta.

Paulo Dybala ya tabbatar da cewa shi da Budurwarsa Oriana Sabatini su na dauke da wannan cuta. ‘Dan wasan na Juventus Dybala ya bayyana wannan ne a shafinsa na Instagram jiya.

Dybala mai shekara 26 a Duniya ya na soyayya ne da Oriana Sabatini, 'Diya wurin wani tsohon ‘Dan wasan Duniya. Dukkaninsu yanzu su na dauke da wannan cuta inda ake kula da su.

Haka zalika kungiyar Milan ta fitar jawabi da ya nuna cewa Darektanta Paolo Maldini da kuma ‘Dansa Daniel Maldini duk sun kamu da wannan cuta, kuma tuni an killace su a gida.

KU KARANTA: Blaise Matuidi ya kamu da cutar Coronavirus - Juventus

Cutar Coronavirus ta kama Maldini, Dybala da Fellaini a Italiya da Sin

Marouane Fellaini ya dauko cutar Coronavirus a Garin Jinan
Source: Getty Images

Kungiyar AC Milan a jawabin na ta, ta ce za a cigaba da kula da Maldini mai shekaru 51 da Matashin ‘Dan wasa Daniel Maldini, har sai zuwa lokacin da aka tabbatar sun samu lafiya.

A yau Lahadi, 22 ga Watan Maris, 2020 ne mu ka kuma samu labarin na cewa ‘Dan wasa Marouane Fellaini ya shiga cikin sahun wadanda su ka kamu da cutar COVID-19 a China.

Tsohon ‘Dan wasan Manchester United da Everton Marouane Fellaini ya na taka leda ne a kungiyar Shandong Luneng. Rahotanni sun ce shi ne ‘Dan kwallon farko da ya kamu da cutar.

Yanzu haka dai wannan cuta da ta fara bayyana a Yankin Wuhan a Sin, ta yi kamari a kasar. Haka zalika dubunnan mutane sun kamu da cutar mai kawo wahalar numfashi a Italiya.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit Newspaper

Online view pixel