Da duminsa: An rufe tashar jirgin kasan Abuja-Kaduna

Da duminsa: An rufe tashar jirgin kasan Abuja-Kaduna

Hukumar jiragen kasan Najeriya ta dakatad da jigilar fasinjoji a jiragen kasanta na Abuja zuwa Kaduna, Legas zuwa Ibadan da sauran sassan tarayya.

Mataimakin kakakin hukumar, Yakubu Mahmoud, ya bayyana hakan ne a jawabin da ya saki ranar Asabar, 21 ga Maris, 2020.

Yace “Hukumar jiragen kasan Najeriya ta yanke shawarar dakatad da jigilar fasinjoji fari daga ranar Litinin 23 ga Maris, 2020.“

“An yanke shawarar ne sakamakon yaduwar cutar Coronavirus“

“Za a sanar da fasinjoji duk lokacin da aka canza shawara.“

Da duminsa daga kotun koli: An rufe tashar jirgin kasan Abuja-Kaduna

Da duminsa daga kotun koli: An rufe tashar jirgin kasan Abuja-Kaduna
Source: Twitter

A bangare guda, Ministan lafiya, Dakta Osagie Ehanire, ya bayyana cewa an samu karin mutane 10 da suka kamu da cutar Coronavirus a Najeriya.

Ministan ya bayyana hakan ne a shafinsa na Tuwita ranar Asabar, 21 ga watan Maris, 2020.

Yayinda bakwai aka samu a Legas, sauran ukun na birnin tarayya Abuja.

Yanzu dai akwai jimillar masu cutar 22 a Najeriya kuma an sallami biyu da suka samu sauki.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel